Rundunar ’Yan Sanda a Kasar Ghana ta sanar da cafke shahararren mawakin kasar, Shatta Wale, bayan ya yada labarin karya a shafin sada zumunta cewar wasu mutum biyu sun harbe shi.
Mawakin shi ne ya mika kansa wajen ’yan sanda bayan an bayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bayan gano labarin da ya yada ba gaskiya ba ne.
- An yi garkuwa da masunta 13 a kan hanyar zuwa kamun kifi
- BUK za ta fara yin takin zamani da iskar gas daga dagwalon masana’antun fata
A cikin wata sanarwar da rundunar ta Ghana ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce bayan sun bayyana mawakin da wasu mutum biyu yaransa a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo ne, mawakin ya mika kansa.
Har wa yau, sanarwar ta kara da cewa an cafke shi ne don ya taimaka wa ’yan sanda a binciken da suke gudanarwa kan zarginsa da yada labarin bogi.
Tuni rundunar ’yan sanda a kasar ta fitar da sanarwa tana gargadin mutanen kasar game da yada labaran karya, don guje wa tashin-tashina.
Ko a watannin baya, wani malamin addinin Kirista ya yi harsashen cewa za a kashe mawakin a ranar 18 ga watan Oktoban 2021.
Sai dai Shatta ya bayyana cewar gaza ba shi kariya da jami’an tsaro suka yi, shi ne ya sa shi yada labaran karyar don jan hankalinsu game da halin da yake ciki.
Sai dai tuni shi ma malamin Kiristan da ya yi hasahen mutuwar mawakin ya shiga hannun jami’an tsaron.
Mutane da dama ne dai suka shiga tafka muhawara kan dalilin da yasa mawakin ya aikata hakan, wasu kuma daga cikin masoyan mawakin na goyon bayansa musamman a shafukan sada zumunta.