A yayin da Musulmi ke Mauludin zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW), Shugaba Tinubu ya roki shugabannin addini su yi wa mabiyansu nasiha kan koyi da halayen Annabi Muhammad (SAW).
A sakonsa na Mauludi, Tinubu ya jaddada muhimmancin nasiha kan bin koyarwar Manzon Allah (SAW) sau da kafa, da kuma yi wa Najeriya da shugabanni a dukkanin matakai addu’o’in domin samun cigaba mai dorewa kasar.
- Gwamnatin Kano za ta yi karar alkalin zaben gwamna kan cin mutuncin Kanawa
- DAGA LARABA: Dalilin da ba za mu bari likita na miji ya duba matanmu ba
Sanarwar da kakakinsa, Ajuri Ngelale, ya fitar ta ce, “a yayin da gwamanti ke daukar matakan bunkasa tsaro da tattalin arzikin Najeriya, akwai bukatar goyon baya da kishi da haukuri daga ’yan kasar. Da yardar Allah sauki na nan tafe.
“Ya kamata Musulmi su yi tsayuwar daka wajen dabbaka koyarwar Annabi Muhammad (SAW) wajen ibada da jin tsoron Allah, juriya da kankan da kai da sadaukarwa da kuma kyakkyawar mu’amala.”
Tinubu ya kuma bukaci su yi amfani da lokacin Mauludi wajen taimakon mabukata da masu rauni.
Sakon Kashin Shettima
A nasa sakon, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya bukaci ’yan Najeriya su yi amfani da lokacin Mauludi wajen zurfafa tunani kan halin da kasar ke ciki da kuma mafita mai dore da take bukata.
Ya roke su da su guji debe kauna da Gwamnatin Tinubu, saboda tana yin shirye-shiryen inganta rayuwarsu, “da shawo kan duk kalubalen da kasar nan ke fuskanta, don ta samu ci gaba da karin martaba a idon duniya.”
Atiku Abubakar
Shi kuma a sakonsa, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, rokon malamai ya yi da su yi amfani da matsayinsu wajen kira ga al’umma su zauna lafiya.
Atiku, ta hannun kakakinsa, Paul Ibe, ya kirayi Musulmi su yi koyi da rayuwa Manzon Allah (SAW) da dabi’unsa na rikon amana da juriya da kyautatawa da kuma zaman lafiya.
Ya bukaci ’yan kasar “kada su yanke kauna saboda matsalolin da take ciki, su hada kai wajen gina ta domin ci gabansu ta hanyar kaunar juna da son zaman lafiya.”
Shugaban Majalisa
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da mataimakinsa, Barau Jibrin, su ma sun yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi koyi da dabi’un Manzon Allah (SAW) na hakuri da juriya da zaman lafiya, domin samun aminci da cin ma muradun kasa.