Amirul Muminina Ali bin Abi Talib ya ce: “Falalar Allah tana tabbata ta hanyar yi maSa godiya, yi wa Allah godiya yana kawo karin albarka, karin albarka ba zai yanke ba yana zuwa daga Allah har sai mutum ya daina godiyar. Idan Musulmi yana kan wani matsayi mai kyau a wurin Allah kuma ya tsare amanar wannan matsayi tare da gode wa Allah, Allah zai ba shi matsayin da ya fi wannan, amma idan ya nuna rashin godiya, Allah zai sanya wannan albarka ta zame masa tarko.”
Alhasan ya ce: “Idan ka ga Ubangijinka Yana saukar maka da albarka (kamar yana ba ka dukiya) a lokacin da kake saba maSa, to ka yi taka-tsantsan. Domin Allah Madaukaki Ya ce: “Da sannu za Mu kama su ta inda ba su sani ba.” (k:7:182). A kan wannan aya Sufyan ya ce: “Allah zai yi ta ba su dukiya ko saukar musu da albarka, a lokacin da kuma zai hana su yi musu godiya.” Kuma Allah Yana kyamar wadanda ba su gode maSa daga cikin bayinSa. Ya ce: “Lallai nemutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.” (k:100:6).
’Yan uwa Musulmi! Ta hanyar nuna godiya ga Allah da yi maSa da’a ne kofofin alherai suke budewa ga mutum a nan duniya da kuma Lahira. “Kuma da lallai mutanen alkaryu sun yi imani kuma suka yi takawa, da hakika Mun bude albarkoki a kansu daga sama da kasa…” (k:7:96).
Yi wa Allah godiya yana iya kasancewa da baki (harshe) ko da zuciya ko da sauran gabbai. Gode wa Allah da harshe yana nufin yi maSa yabo kan dimbin alheransa. Yi wa Allah godiya da harshe babbar hanya ce ta nuna wa Allah godiya kuma hakan yana daga cikin ayoyi na farko da aka saukar a cikin Alkur’ani Mai girma.
Yi wa Allah godiya da hannuwa na nufi yi amfani da su wajen aikata abin da Allah Yake so da guje wa aikata abin da bai so. Yi wa Allah godiya da ido na nufi kada mutum ya yi amfani da su wajen kallon haram; yi wa Allah godiya da harshen a nufin mutum ya fadi gaskiya kawai; godiya ga Allah da kunne a guji amfani da su wajen sauraren zunde da annamimanci da cin zarafin wani da sauran haramtattun abubuwa. Kuma Allah Ya yi umarni da a gode wa iyaye. Ya ce: “Ka gode Mini da kuma mahaifanka.” (k:31:14).
Daga cikin alamomin godiya ga iyaye akwai yi musu hidima da dadada musu da tausaya musu da kankan da kai gare su. Zunubi ne a yi musu rashin kirki ko a saba musu a cikin duk wani abu da bai saba wa dokokin Musulunci ba. Mafi alherin mutane shi ne wanda ya yi amfani da falalar Allah wajen neman Lahira, mafi sharrin mutane shi ne wanda ya karkatar da falalar Allah wajen sabo da bin da rude-ruden duniya. Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai Allah, hakika, Ma’abucin falala ne a kan mutane, kuma amma mafi yawan mutane ba su godewa.” (k:40:61).
’Yan uwa masu girma a cikin imani! Yin godiya daya ne daga cikin siffofin Ubangijimmu kuma mafi soyuwa gare Shi daga bayinSa shi ne mai yin godiya. Kuma wanda Ya fi ki shi ne wanda bai da godiya. Don haka Allah mai cikakkiyar godiya ne kuma yana son godiya. Ka gode wa duk wanda ya kyautata maka a tsakanin mutane wani bangare ne na yi wa Allah godiya. Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ba ya gode wa mutane, ba zai gode wa Allah ba.” (Ahmad ya ruwaito).
Duk da haka idan ka yi alheri ga wani, kada ka sa ran sai ya gode maka. Idan kana taimakon wani kada ka sa ran ya yi maka wani abu, in ka yi haka kana kasuwanci ne ba taimako ba. Don haka ka nemi lada a wurin Allah, kuma ka nuna gamsuwa da duk abin da Allah Yake ba ka, sai ka kasance mafi godiyar mutane. Ka gode wa Allah ka tsarkake da tuna Shi da yawa, domin wannan ne mafi girman aikin ibada. Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya ci daga arzikin Allah sannan ya gode maSa, kamar mai yin azumi ne kuma mai hakuri.” (Buhari). Duk wanda bai godiya kan kananan alherai ba zai yi godiya kan many aba. Lokacin da aka tambayi Abu Mughira cewa: “Yaya ka wayi gari?” Sai ya ce: “Mun wayi gari cikin dimbin alherin Allah, amma mun kasa yi maSa godiya.” Mutane kashi biyu ne: wanda aka jarrabe shi da wadata domin a ga yadda zai yi godiya da wanda aka jarrabe shi da abin ki domin a ga yadda zai yi hakuri. Don haka dan uwa ka yi kokari ka hada hakuri da godiya domin ka kasance daga cikin bayin Allah masu bauta maSa na gaskiya.”
Imam Murtada Muhammad Gusau, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Nagazi-Ubete da ke Okene, Jihar Kogi ya gabatar da wannan Huduba ce a ranar 21 ga Jimada Akhir, 1436 Bayan Hijira daidai da 10 ga Afrilu, 2015, kuma za a iya samunsa ta: 08038289761 ko [email protected]