Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu, Bawan Allah Muhammad, tare da alayensa da sahabbansa baki daya da kuma duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, idan an lura da inda muka kwana, za a ga mun tabo batun riya, wadda take kishiya ce ta ikhlasi. Mun tsakuro magana cewa tana shiga cikin ayyukan salihan bayin Allah, kuma ta fi ban tsoro gare su da fitinar Dajjal. Yau ga ci gaba:
Abin da ba riya ba ne:
Duk wanda ya aikata wani aikin ibada mai kyau kuma don Allah kadai (wato ya yi ikhlasinsa), sannan Allah Ya jefa yabon kirki a kansa a cikin zukatan muminai, alhali shi bai bukaci haka daga gare su ba, amma sai ya yi farin ciki da falalar Allah, kuma ya yi bushara da haka, to, wannan ba zai cutar da shi ba. Wannan ba ya cikin riya, saboda bai yi nufin mutane su gani ko su ji su yaba masa ba.
Abu Zarri (Allah Ya yarda da shi), yana cewa, ‘An tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), dangane da mutumin da yake aikata wani aikin alheri, wanda mutane suke gode masa (suke yabonsa) a kan aikin?’ Sai ya ce, “Wannan wata bushara ce da aka gaggauta wa mumini.” Muslim ne ya ruwaito shi. Amma wanda ya aikata wani aikin kwarai, kuma ya kawata shi don mutane su yaba masa, to wannan babu makawa riya ne.
Ukubar mai riya:
Burin mai riya ya wofinta, kuma aikinsa ya tabe, sannan nufinsa ya rushe. Za a yi masa ukuba guda biyu – ta duniya da kuma ta Lahira.
Ukubar duniya: Allah Zai kunyatar da shi, Ya yaye suturarsa (a tsiraita shi), Ya bayyanar da boyensa. Manzon Allah, mai tsira da amincin Allah, yana cewa, “Duk wanda ya jiyar (ya yi don a ji – sum’a), Allah Zai yi sum’a da shi; duk wanda ya yi riya, Allah Zai yi riya da shi.” (Ko kamar yadda Manzon Allah ya fadi). Muslim ne ya ruwaito Hadisin. Malam Khaddabiy (Allah Ya jikansa), ya ce, “Ma’anar wannan (Hadisi) shi ne, wanda ya aikata wani aiki na ibada ba a kan ikhlasi ba, sai dai yana nufin mutane su gan shi kuma su ji shi, to, za a yi masa sakamako a kan haka. Allah Zai shahara shi (Ya mayar da shi wani gwarzo, ya yi fice a tsakanin al’umma) daga nan sai Ya tozarta shi, Ya fito da abin da ya kasance yana boyewa a fili (kowa ya gane cewa ashe dai da ma wani holoko ne – Allah ne Mafi sani). Har ma dai ta yadda ko da mai riya ya tattara abin da yake boyewa a ransa ko wanda yake boyewa a cikin kirjinsa, to, lallai Allah Zai bayyanar da shi. Shi ya sa ma Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), yake cewa, “Wanda ya koshi da abin da ba a ba shi ba, ya yi kama da wanda ya sanya tufafi biyu na zur (karya).” Wato – Allah Shi ne Mafi sani – ga rashin abin da ba a ba shi ba, ga karyar koshi, ba wan ba kanen).
Ukubar Lahira: Mai riya, wanda aka yi wa alkawari ne da wutar Jahannama. Allah Mai girma da daukaka Ya ce, “Wanda ya kasance ya yi nufin rayuwar duniya da kawace-kawacenta, Muna cika musu ayyukansu zuwa gare su a cikinta, kuma a cikinta ba za a rage (musu) komai ba.” Surar Hud, aya ta 15.
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), a cikin Sahihi Muslim, yana cewa, “Farkon mutane, wanda za yi wa hisabi shi ne … sai ya ambata: Wanda ya yi shahada da makarancin Alkur’ani da kuma mai sadaka da dukiyarsa, wadanda suka kasance ayyukansu ba don Allah ba ne, sai a ce wa kowanensu, ‘karya kake yi, sai dai ka yi ne don a ce maka ‘kaza’ kuma an ce din. Saboda haka sai a yi umurni a ja shi a kan fuskarsa har a jefa shi cikin wuta.”
Saboda haka shi mai riya, a duniya wanda ake tozartawa ne; a Lahira kuma a azabtar da shi. Allah Ya kiyashe mu da sharrin riya da sum’a (jiyarwa), amin!
Neman duniya da addini:
Addini (Musulunci) ya fi karfin a ja shi cikin kazantar duniya. Aikin birru (duk aikin da ake yaba kyansa), ba ya tsayuwa kyam ya tabbata, dole sai yana tare da ikhlasi. Duk wanda ya sarrafar da aikin Lahira don samun duniya, sai an yi masa ukuba da shi.
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), yana cewa, “Duk wanda ya yi wani ilimi da ake nufin Allah da shi, sai dai bai yi ilimin don haka ba, sai don ya samu wani abin duniya, to ba zai ji kanshin Aljannah ba Ranar kiyama.” Imam Ahmad da Abu Dawuda ne suka ruwaito shi.
Shi aikin kwarai, ko da ya kasance mai yawa ne amma yana tare da batacciyar niyya, yana gangarar da ma’abucinsa zuwa ga halaka. Lallai Allah Ya bayar da labarin munafukai cewa su suna Sallah, suna ciyarwa, suna jihadi. Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bayar da labarinsu cewa suna karanta Littafin Allah (Alkur’ani) a cikin fadinsa, “Misalin munafuki da yake karanta Alkur’ani kamar itaciyar raihana ce, tana da kamshi, amma ’ya’yanta daci.” Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi. Lallai gaskiyar niyyarsu cikin tsarkake aiki don Allah ta bace. Kuma Allah Ya ce, a game da su, “Lallai ne munafukai suna a magangara mafi kaskanci daga wuta. Kuma ba za ka sama musu mataimaki ba.” Surar Nisa’i, aya ta 145.
Farkon wadanda za a kone su da wuta shi ne mai karatun Alkur’ani da mai jihadi da mai sadaka da dukiyarsa, wadanda ayyukansu ba su kasance tsintsar gaskiya (ikhlasi) saboda Allah ba, sai dai sun yi don a ce wane makaranci ne; wane jarumi ne; wane mai kyauta ne.
Saboda haka ka nemi abin da ke wajen Allah kadai da ayyukanka, domin Shi ne tabbatacce, duk wanda ba Shi ba, mai karewa ne. Idan bawa ya yi aikin alheri yana nufin wani abu na duniya, to, wannan wani yanki ne na aikin munafunci. Ibnu Rajab, a littafin Jami’ul Ulum Wal-Hikam, mujalladi na 2, shafi na 493, yana cewa, “Yana daga cikin mafi girman aikin munafunci, mutum ya yi aikin alheri yana bayyanar da kyakkyawan nufi a kansa, amma sai ya kasance ya yi shi ne don neman wata bukata ta daban batacciya, sai kuma a cika masa ita a haka. Sai ya kai ga wannan manufa, kuma ya yi farin ciki da makircinsa da makarkashiyarsa, sai mutane su gode masa kan abin da ya bayyanar, kuma sai ya sadu da abin da ya yi nufi da shi na abin da ya boye. Irin wannan lallai Allah Ya yi bayaninsa a Alkur’ani dangane da aikin munafukai da Yahudawa.”
Wanda duk ya so yabo a kan abin da bai aikata ba, lallai yana tare da kyacewa ta wuta. Allah Mai girma da daukaka, Yana cewa, “Kada lallai ka yi zaton wadanda suke yin farin ciki da abin da suka bayar, kuma suna son a yabe su da abin da ba su aikata ba. To kada lallai ka yi zatonsu da tsira daga azaba. Kuma (lallai) suna da azaba mai radadi.” Surar Ali-Imran, aya ta 188.
Wannan shi ne karshen mukalar matsayin ikhlasi a Musulunci, sai mu yi ta rokon Allah Ya taimaka mana, Ya sa mu yi ikhlasi a ayyukanmu na ibada, Ya tsare mu daga riya da sum’a, Amin.
Wassalamu alaikum wa rahmatullah!!