Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu, Bawan Allah Muhammad, tare da alayensa da sahabbansa baki daya da kuma duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, yau kuma mukalarmu za ta ci gaba ne kan sinadarai ko makaman da ake tunkude Shaidan wajen tabbatar da ikhlasi a cikin ayyukan ibada. Mun gabatar da bayani kan makamai biyu wato yin addu’a da kuma boye aikin ibada, to yanzu ga:
3. DUBAN AYYUKAN SALIHAN BAYI DA SUKA FI KA: Dangane da ayyukanka na kwarai, kada ka rika duban na mutanen da ke zamaninka ma sam, wadanda suke ba su kai kamarka wajen ayyukan alheri ba, wato wadanda kake gwagwarmayar da su, kuna tsere a cikinsu. A koyaushe ka kasance kana hasashen ayyukan annabawa da salihan bayin Allah magabata. Allah, Wanda tsarki ya tabbatar maSa, Yana cewa, “Wadancan ne Allah Ya shiryar, saboda haka ka yi koyi da shiriyarsu. Ka ce, “Ba ni tambayarku wata ijara (ba ni bukatar ku biya ni, don na kawo muku Alkur’ani). Shi (Alkur’ani) bai zama ba face tunatarwa ga talikai.” (An’aam, aya ta 90).
Haka nan kuma ka rika karanta tarihin salihan bayin Allah na daga malamai da masu yawaita bautar Allah da manyan mutane masu daraja da wadanda suke da zuhudu (gudun duniya). Yin wannan, al’amari ne da ake kwadaituwa da shi wajen karuwar imani a cikin zuciya, musamman saboda irin karsashin da suke bayarwa, in an karanta.
Lallai zuciya tana kwadaituwa ta zaku ta kuma motsa cikin nishadi da bukatuwa ga yin irin abin da magabata suka yi wajen kara kusanta zuwa ga Mahaliccinsu, a duk lokacin da ta ji yadda suka yi ta gwagwarmaya a rayuwarsu a kan haka. Ita zuciya tana bukatar haka, musamman idan ta rika jin wadansu bayanai da ba safai take ganin irinsu a zamaninta ba. Saboda haka, sai an mayar da hankali an jajirce, sannan ake samun abin da ake bukatar a kai gare shi na samun sa’ada (daukaka da cin nasarar rayuwa zuwa ga shiga Aljanna).
4. YA KASANCE KANA RAINA AYYUKANKA NA IBADA: Asara ko cutar bawa tana tattare da yardarsa da amincewarsa ga kansa, wato ya sakankance da abin da yake kansa. Duk wanda ya yi dubi da ransa, kuma ya sakankance, ya yarda ya jinjina wa ran nasa, to lallai ya halaka shi (ran). Kuma lallai wanda ya yi dubi da ayyukansa na ibada da dubi na mamaki da yabo, to za ka iske ikhlasi ya yi karanci a wurinsa, ko kuma ikhlasin ya sabule masa, ya bar shi, ba ya tare da shi gaba daya, ko kuma ya bata aikin kwarai bayan ya aikata shi.
Sa’idu bin Jubairu, (Allah Ya yarda da shi), yana cewa, “Wani mutum ya shiga Aljanna da sabo, kuma wani mutumin daban ya shiga wuta da kyakkyawan aiki.” Sai aka ce masa, “Yaya haka zai kasance?” Sai ya ce, “Wancan mutumin ya aikata sabo, amma bai gushe ba yana tsoron ukubar Allah a kan wancan aikin sabo da ya aikata, har sai da ya sadu da Allah, sai Allah Ya gafarta masa saboda tsoron da yake wa Allah Ta’ala a kan haka; shi kuma mutumin da ya aikata kyakkyawan aiki, bai gushe ba yana kambama kansa, yana mamakin kansa game da aikin, yana yabon kansa, har sai da ya sadu da Allah, sai Allah Ya shigar da shi wuta.”
Shi ya sa mutum lallai ya kasance bai sakankance ba, bai amince wa kansa ba, komai yawan ayyukan alherin da yake yi, sai dai ya zamo mai yawan kwadayi wajen samun rahamar Allah kuma yana tsoronSa dangane da azabarSa; dabi’ar da annabawan Allah suke kanta ke nan!
5. TSORON RASHIN KARbUWAR AYYUKAN IBADA: Ka kasance duk wani aikin alheri da ka aikata shi, to ka raina shi, wato ya zamo ba ka dauke shi a bakin komai ba. Hasali ma dai ya kamata, idan ka aikata aikin, ka zama mai tsoron rashin karbuwarsa. Lallai ya kasance daga addu’ar magabata na kwarai tana cewa, “Ya Allah, muna rokon Ka taimake mu yin aiki na kwarai, kuma Ka kiyaye mana shi.”
Yana daga cikin abin da ke kiyaye aikin ibada, ya tsare shi, mutum ya daina ganin girman aikin da yin alfahari da shi, sai dai ya kasance koyaushe yana tsoron rashin karbuwarsa. Allah, Wanda tsarki ya tabbatar maSa Yana cewa, “Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a bayan tukka, ya zama warwararku, kuna rikon rantsuwoyinku domin yaudara a tsakaninku, domin kasancewar wata al’umma ta fi riba daga wata al’umma. Abin sani kawai Allah Yana jarrabar ku da shi, kuma lallai ne Yana bayyana muku a Ranar kiyama, abin da kuka kasance, a cikinsa, kuna saba wa juna.” (Nahli: aya ta 92).
Ibn Kasir yana cewa, a cikin tafsirinsa, mujalladi na 3, shafi na 248, “Manufa, suna bayar da abin bayarwa (na kyauta) alhalin suna tsoro cikin firgicin cewa ba za a karba musu ba; saboda tsoron kada abin ya kasance sun takaita, sun gaza wajen tsayar da sharadi ko sharuddan da aka gindaya wajen bayar da abin bayarwar.”
Imam Ahmad da Tirmizi sun ruwaito daga Uwar Muminai A’isha, (Allah Ya yarda da ita), ta ce, “Ya Manzon Allah, (shin wannan aya), “Da wadanda ke bayar da abin da suka bayar, alhali kuwa zukatansu suna tsorace domin suna komawa zuwa ga Ubangijinsu.’ (Mu’minun: aya ta 60), shi ne mutumin da ya yi sata; ya yi zina; ya sha giya; alhalin yana tsoron Allah, Mai buwaya da daukaka?”
Sai Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “A’a, ya ke diyar Abu Bakar Assiddik, yadda al’amari yake, su ne wadanda suke Sallah; suke yin Azumi; suke bayar da sadaka, alhali suna tsoron kada a ki karba musu (wadannan ayyukan).”
Shi ikhlasi yana bukatar matukar kokari da jajircewa da karfin niyyar yi don Allah kafin a fara aikin ibada da kuma lokacin da ake tsakiyar yin sa da kuma bayan an kammala shi.
Saboda haka lallai ne mutum ya kasance kowane lokaci yana fadake, yana sanin abin da yake gabatarwa na ayyukan ibada, kuma tunaninsa da motsinsa yana damfare da cewa Allah kadai ake yi wa aikin, alhali yana da masaniyar yana gudanar da aikin a karkashin koyarwar Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), sannan kuma ya mayar da al’amari ga Allah, ya sanya rai cewa Allah din Ya karba.
Idan an lura sosai, yau darasin namu da ya soma tun daga duban ayyukan salihan bayi da suka fi ka; da cewa mutum ya kasance yana raina ayyukansa na ibada; sannan ya rika jin tsoron rashin karbuwar ayyukan ibada, za a fahimci cewa komai sakar wa Allah ake yi sai yadda Ya yi, sai yadda Ya ga dama.
Muna fata Allah Ya yi mana muwafaka da abin da yake daidai da abin da Yake so. Nan za a sa aya, sai kuma darasi na gaba, in Allah Ya kaddara saduwarmu.
Wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuh!