Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya kalubalanci hukumar Hisbah ta jihar Kano game da ‘Black Friday’.
A ranar Juma’a hukumar ta gargadi dukkan ’yan kasuwa da su gujewa amfani da kalmar ‘Black Friday’ wajen tallar kayayyakinsu.
- Hisbah ta hana ‘Black Friday’ a Kano
- Jami’an Hisbah sun samu horo kan damben Karate a Kano
- An dakatar da kwamandan Hisbah da ake zargi da karkatar da tallafin COVID-19 a Kano
Shehu Sani ya ce hakan da hukumar ta yi shirme ne, inda ya ja hankalin ta da ta mai da hankali wajen kashe-kashe da garkuwa da ake yi a yankin Arewacin Najeriya.
Ya kara da cewa, ranar Juma’a babbar rana ce ga musulmai, amma yana ganin cewa babu komai dan an kira ta da wani suna.
Shehu Sani ya kara da cewa an fi bukatar Jami’an Hisbah a filin daga, inda ya kamata a ce sun magance matsalar tsaro da ta addabi yankin arewa.