✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsalar tsaro: PDP ta kalubalanci Buhari kan kalaman Ndume

Kwamitin Majalisa na zargin gwamnati da rashin wadata sojoji da kudade

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci fadar shugaban kasa da ta ba da amsa kan kalaman Shugaban Kwamitin Sojin Kasa na Majalisar Dattawa Sanata Ali Ndume, cewa kin bayar da isassun kudaden gudanarwa da gwamnatin ke yi shi ne ummul-haba’isun matsalar tsaro a Najeriya.

PDP ta kuma yi kira ga Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina da ya wanke kansa daga zargin alaka da ‘yan bindigar da suka addabi jihar, saboda abin da ta kira yunkurin gwamnan na siyasantar da lamarin.

Rahotanni dai sun ambato Sanata Ndume ranar Talata na zargin Gwamnatin Buhari da gaza bai wa sojojin isassun kudade a matsayin dalilin da yake kara ta’azzara matsalar tsaro a kasar.

Jam’iyyar a wata sanarwa da kakakinta, Kola Ologbondiyan ya fitar ta ce, “Akwai bukatar gwamnatin ta wanke kanta daga zargin, saboda karuwar matsalar ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da ta’addanci na nuna gazawarta ta takowacce fuska.

“Abin takaici ne matuka yadda gwamnatin ta gaza cika kusan dukkannin alkawuran da ta yi wa ‘yan kasa a bangaren tsaro musamman kan cire manyan hafsoshin tsaron da kuma sauya fasalin tsaron kasar”, inji PDP.

Kazalika, jam’iyyar ta kuma nuna takaicinta kan yadda gwamna Masari na Katsina ya koma zargin ‘yan siyasa kan matsalar tsaron jiharsa, tana mai cewa bayan a zahirin gaskiya gwamnan ya san ‘yan bindigar saboda ya sha tattaunawa da su a baya.

Daga nan kuma ta shawarci gwamnan da ya mayar da hankali wajen gano bakin zaren matsalar tsaron jihar, saboda a cewarta, babu wasu ‘yan adawa da suke tallafa wa ‘yan ta’adda a jihar ko ma a kowanne bangare na Najeriya.