✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro na dab da zama tarihi a Najeriya – Buhari

Buhari ya ce da sabbin jiragen Super Tucano, matsalar tsaro na dab da zama tarihi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce bayan sayo sabbin jiragen Super Tucano da kuma sauran jiragen yaki da gwamnatin Najeriya ta yi daga Amurka, matsalar tsaro na dab da zama tarihi a kasar nan.

Ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a birnin New York na Amurka yayin ganawarsa da Jakadiyar kasar a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield a gefen taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) karo na 76.

A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Femi Adesina ya fitar ranar Asabar, Shugaba Buhari ya ce tallafin kasar ta Amurka ya kara karfafa gwiwar sojoji da sauran mutanen Najeriya.

Game da batun yadda kasar ta sami nasarar yaki da Coronavirus, musamman sabuwar samfurin Delta, Buhari ya ce, “Mun kafa wani kwamiti na musamman da hadin gwiwar Jihohi sannan muka ilmantar da mutane a kan matakan kariya, kuma in aka yi la’akari da yawan jama’armu, muna tabukawa sosai gaskiya.”

Da take nata jawabin, Ambasada Linda ta ce kusan kaso 70 cikin 100 na aikinta a majalisar ya fi karkata ne ga nahiyar Afirka, tana mai nuna damuwarta kan sabbin juyin mulkin da aka yi a kasashen Mali da Guinea.

A kan batun sauyin yanayi kuwa, Buhari ya ce sama da mutum miliyan 30 ne matsalar ta shafa a kasashen yankin Tafkin Chadi, wadanda suka rasa hanyoyin sana’o’in noma da su da kuma kiwo.

Hakan inji shi ya tilasta wa da yawa daga cikinsu yin kaura zuwa wasu wuraren don neman mafita.