Majalisar Dattawa ta aike wa Shugaban Kasa Muhamadu Buhari da takardar gayyata domin ya zo ya yi mata bayanin akan ci gaba da kashe-kashe da ke faruwa a Najeriya.
Hakanan ita ma Majalisar Wakilai ta aike wa shugaban da irin wannan goron gayyata, wanda hakan ya sa Majalisar Dattawa ta amince da ganin shugaban a lokaci daya.
Hakanan kuma majalisar ta bukaci shugaban da ya kaddamar da dokar t abaci a jihohin da rikici ke ta kara kamari.
Wannan kuduri ya zo bayan Sanata George Akume ya gabatar da ita a gaban majalisar, bayan an kashe malaman majami’a guda biyu da wasu masu ibada 17 a Jihar Binuwei.