Kusoshin jam’iyyar adawa ta PDP a Majalisar Wakilai sun yi kira ga ’yan Najeriya kan su tursasa wakilansu a Majalisar Dokoki domin su fara yunkurin tsige Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Jagoran ’yan majalisan, Hon. Kingsley Chinda a wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Lahadi ya ce kamata ya yi a tsige shugaban saboda nuna gazawarsa karara da kuma ci gaba da karya tanade-tanaden sashe 14(2) (b) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
- Shirme ne kiran Buhari ya yi murabus —Gwamnatin Tarayya
- Ganduje na bukatar jami’ar Amurka ta nemi afuwarsa saboda ‘damfarar sa’ da matsayin Farfesa
A cewarsu, sashen ya yi tanadin, “Tilas ne Shugaban Kasa ko mataimakinsa ya sauka daga mukaminsa idan kaso biyu cikin uku na mambobin Majalisar Zartarwa ta Tarayya suka amince cewa Shugaban Kasa ko Mataimakinsa ya gaza aiwatar da aikinsa.”
’Yan majalisar sun ce, “Kullum kwanan duniya, ’yan bindiga da ’yan ta’adda na ci gaba da cin karensu ba babbaka ta hanyar kisan mutanen da ba su ji ba, basu gani ba, yayin da su kuma jami’an gwamnati ke ci gaba da wasoso da dukiyar kasa.”
Sun kara da cewa martanin Fadar Shugaban Kasa da na sojoji kan kisan manoma a garin Zabarmari na jihar Borno a kwana-kwanan nan abin Allah-wadai ne, suna masu cewa gwamnatin Buhari tana nuna halin ko in kula da rayuwar ’yan kasa.
“Shugaba Buhari ba shi da niyyar samar da nagartaccen shugabanci da zai ceto kasar daga kokarin durkushewa. A maimakon ya fuskanci matsalolin dake ci wa kasar tuwo a kwarya, ya koma ya harde kafa a fada sai dai kawai ya rika yi wa mutane jaje.
“Muna kira ga ’yan Najeriya da su farkar da wakilansu a Majalisar Dokoki ta hanyar tilasta musu tsige shugaban domin ceto Najeriya,” inji ’yan majalisar.
Sai dai da aka tuntube shi, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar ta Wakilai, Alhasan Ado Doguwa ya bayyana kiran a matsayin wanda ba shi da tushe ballantana makama.
“Rashin kan gado ne wadannan ’yan PDP din mara sa kishin kasa su yi kira da a tsige Buhari a irin wanna lokacin duk da iri rikon sakainar kashin da jam’iyyarsu ta yi wa Najeriya a cikin shekaru 16,” inji Doguwa.