Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce matukar ba a tashi tsaye an magance kalubalen tsaro ba, ba lallai ne Najeriya ta ci gaba da wanzuwa ba nan da shekarar 2023.
Ya ce matsalar tsaron na kuma iya yin barazana ga babban zaben shekarar mai zuwa.
- Duk layin wayar da aka toshe ba za a bude ba sai mai shi ya kawo lambar NIN
- ’Yan bindigar da suka sace jami’in Kwastam a Zariya na neman N100m
Ya bayyana fargabar ce a Abuja, yayin wani taron tattaunawa kan matsalar tsaro da aka shirya ranar Litinin.
Gidauniyar Global Peace Foundation da ta Vision Africa ne suka shirya taron da nufin lalubo bakin zaren matsalar.
Sarkin, wanda daya daga cikin Shugabannin Majalisar Tattaunawa Tsakanin Addinai, Sheikh Kunle Sanni ya wakilta, ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda Gwamnatin Tarayya ta gaza magance matsalar ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ma masu daukar nauyinsu.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce, “An kama mutane da dama saboda zargin ayyukan ta’addanci, amma nawa aka taba daurewa ko aka yanke musu hukunci? Wadannan mutanen fa sun kashe dubban mutane.
“Ya kamata a ce an dauki mataki kan duk wanda sakacinsa ne ya jawo hakan. Kamata ya yi a ce Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro da Manyan Hafsoshin Tsaro duk sun ajiye mukamansu yanzu.
“Muna bukatar sabbin mutane su zo da sabbin dabarun yakar matsalar.
“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya san yadda zai dauko mutanen da za su yi masa aiki, amma bai san yadda zai kore su ba.
“Muddin ba mu tashi tsaye mun fada wa junanmu gaskiya ba, to ba lallai ne Najeriya ma ta kai nan da 2023 ba. Allah Ya kiyaye, ba na fatan haka.
“Gwamnati ta fada mana cewa ta san masu hannu a cikin matsalar tsaro, matukar za a kawar da son zuciya a fara yanke wa ’yan ta’adda hukunci, da yawa daga cikinsu za su iya canza tunani. Amma abin takaicin shi ne mutane kamar sun mayar da matsalar tsaro hanyar samun kudi,” inji Sarkin Musulmin.