✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsalar tsadar kayan abinci duk duniya ce ba iya Najeriya ba – Lai Mohammed

Ya ce masu wasa da hankulan mutane ne ke kokarin nuna a iya Najeriya matsalar take

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce matsalar tsadar kayan abinci da ta man fetur da ake fama da ita yanzu duk duniya ce ba iya Najeriya kawai ba.

Ya bayyana hakan ne a Abuja, lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Litinin.

A cewarsa, masu yunkurin juya zance ne kawai suke nuna cewa a iya Najeriya ne kawai ake fama da matsalolin.

Ya ce duk ’yan adawa da ’yan jaridar da ke kwatanta farashin kayayyakin kafin 2015 da yanzu, kawai suna neman shafa musu kashin kaji ne.

“Yadda ake juya alkaluman ana yi ne don a karkatar da hankulan mutane. Wannan wasa da hankulan mutane ne.

“Mu dauki farashin kayan abinci da na fetur alal misali, idan ka bincika farashinsu a wasu kasashen, musamman Amurka da Burtaniya, za ka sha mamaki,” inji shi.

Ministan ya kuma ce gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta samu gagarumar nasara a dukkan bangarori, duk kuwa da tarin kalubalen da take fuskanta.

Daga nan sai ya shawarci ’yan Najeriya da su rika yin taka-tsantsan da irin abubuwan da ya kira karairayin da ’yan adawa ke yi musu.