Bankin Duniya ya amince da bai wa ƙasar Togo tallafin dala miliyan 200 don magance matsalar samar da wutar lantarkin da ƙasar ke fama da ita na tsawon watanni.
A daidai lokacin da za a fara babban zaben ƙasar, a ’yan watanni masu zuwa, Togo na fuskantar matsananciyar matsalar rashin wutar lantarki, lamarin da ya haddasa tsadar rayuwa a ƙasar.
- Masu garkuwa sun harbi jarogan APC sun sace ’ya’yansa a Abuja
- Hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.19
Ministan tattalin arzikƙi da kuɗi na Togo, Sani Yaya, ya bayyana farin cikinsu game da samun wannan tallafi.
Kazalika, ya ce kuɗin zai taimaka wajen gina manyan layin wuta wanda hakan zai taimaka wa ’yan ƙasar da ke rayuwa a ƙauyuka wajen samun wutar cikin sauƙi.
Ministan, ya ƙara da cewa tallafin zai sa sama da mutane miliyan ɗaya da rabi su samu wutar lantarki mara katsewa.
Matsalar ƙarancin wutar da aka fuskanta na zuwa ne, bayan Najeriya ta daina bai wa Togon da Nijar da kuma Benin lantarki ta bayyana taƙaita adadin wutar da za ta dinga ba su a ranar 1 ga watan Mayu, 2024.
Hukumar da ke kula da wutar lantarkin ta ce Najeriya wacce ita ce ta fi ba su wutar na bin su bashin miliyoyin daloli na lantarkin da suka sha kuma suka kasa biya.