✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matawalle ya zama jagoran APC a Zamfara

An mika wa Matawalle tutar jam’iyyar APC yayin gangamin da aka gudanar a Gusau.

Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, ya ayyana Gwamna Muhammad Bello Matawalle a matsayin sabon jagoran jam’iyyar APC a Jihar Zamfara kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanada.

Buni ya bayyana hakan ne yayin mika tutar jam’iyyar ga Gwamna Matawalle yayin wani gangami na karbarsa da aka gudanar a Gusau, babban birnin Jihar.

A yammacin Talata ne Gwamnan na Zamfara, ya sauya sheka daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulkin kasar.

Gabanin sauyin shekar da Gwamna Matawalle ya yi, tsohon Gwamna Abdulaziz Abubakar Yari ne shugaban jam’iyyar a Jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, taron ya samu halarcin tsaffin gwamnonin Jihar da suka hada da Ahmed Yarima, Mamuda Aliyu Shinkafa da shi Yarin kansa.

A yayin taron ne Gwamna Matawalle ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, yana mai bayyana gazawar da jam’iyyar ta yi wajen shimfida kyakkyawan tsarin da zai ciyar da Jihar Zamfara gaba da kuma kasa baki daya.

Bayanai sun ce guguwar sauyin shekar da ta kada da Gwamna Matawalle ta hada da dukkan Sanatoci uku na Jihar da kuma shida daga cikin bakwai na masu wakiltar Jihar a Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Daga cikin wadanda suka halarci akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Ministan Muhalli, Muhammad Mahmoud, Ministar Harkokin Jin Kai, Sadiya Umar-Faruk da kuma Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu.

An dauki tsawon lokaci ana rade-radin cewa gwamnan zai jam’iyyar APC, inda gabanin gabanin haka wasu gwamnonin jam’iyyar suka taro a Kaduna domin lallashin tsohon Gwamna Yari.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, Gwamnonin sun taru a gidan tsohon Gwamnan domin neman goyon bayansa dangane da babban kamun da jam’iyyar ta su za ta yi.fara.

Gwamonin da suka yi taron sun hada da na Jihar Yobe, Mai Mala Buni, Malam Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, Yahaya Bello na Jihar Kogi, Badaru Abubakar na Jigawa da kuma Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu.