✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matawalle ya bar N20bn a lalitar Gwamnatin Zamfara — APC

APC ta bayyana cewa sabon Gwamnan Zamfara ba shi da alkibla.

Jam’iyyar APC mai adawa a Jihar Zamfara ta yi ikirarin gwamnatin Muhammad Bello Matawalle ta bar wa sabuwar gwamnatin PDP, karkashin Gwamna Dauda Lawal Dare kimanin naira biliyan 20.5 da kuma dala miliyan 1.9 a lalitar gwamnati.

APC cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaranta, Yusuf Idris Gusau ya sanyawa hannu, ta zargi sabuwar gwamnatin da musanta karbar kudaden.

Ta kuma mayar wa da sabuwar gwamnatin martani kan zargin tsohon gwamna, Matawalle da sama da fadi da wasu motocin alfarma wadanda ta ce an raba su ne ga amfanin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar.

Tun farko dai gwamnatin Jihar Zamfara ta bai wa tsohon Gwamna Muhammad Bello Matawalle wa’adin kwanaki biyar da ya bayar da bahasi kan motocin alfarma masu sulke na biliyoyin naira da aka sayo daga asusun gwamnatin jihar, kuma suka yi batan-dabo.

A cewar sanarwar, “idan har sun tashi tabbatarwa, muna sa ran za su hada kai da ma’aikatu da hukumomin gwamnati domin sanin inda motocin suke a maimakon damun Matawalle wanda tuni ya ci gaba da tafiyar da rayuwarsa.

Sanarwar ta kuma bayyana sabon gwamnan a matsayin wanda ba shi da alkibla.

Ta kuma karyata zargin cewa tsohon gwamnan bai mika takardun da ya kamata ba kafin barin mulki tana mai cewa “babu wani tsohon gwamna da zai bar kujerarsa ba tare da mika takardu ba.”

A cewarta, Matawalle ya gabatar da duk wasu takardu ga sabon gwamna karkashin kwamitin karbar mulkin da ya wakilce shi.

APC ta kuma zargi sabon gwamnan da kin nuna damuwa kan kashe-kashe da sace-sacen mutane a jihar da kuma yadda a cewarta ya bar lamuran jihar ya koma halartar taruka a Abuja da Bauchi – wanda ke nuna gazawar gwamnati.