✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya ba ’yan bindiga wata 2 su mika wuya —Matawalle

Da zarar wa’adin ya cika babu wata magana sai ta ragargazar su.

Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya ce Shugaba Buhari ya ba ’yan bindigar Jiharsa wa’adin wata biyu su tuba su mika makamansu ko kuma su yaba wa aya zaki.

Matawalle ya ce ’yan bindigar na da damar rumgumar shirin sulhu da zaman lafiya na Gwamnatin Jihar cikin wata biyun; da zarar wa’adin ya cika babu wata magana sai ta ragargazar su.

“A ci gaba da matsa kaimi don kawo karshen ayyukan ’yan bindiga don samar da dawwamammen zaman lafiya a jihar, an ba su biyu daga yau, su rungumi shirin zaman lafiya tare da mika makamansu ga gwamnati,” inji shi.

Da yake jawabi kan matakan da Gwamnatin Jihar da ta Tarayya ke dauka don magance matsalar tsaro a Jihar, Matawalle ya ce Buhari ya tura karin sojoji 6,000 zuwa Jihar kuma nan gaba kadan za su fara aiki.

“A tattaunawata da Shugaba Buhari da Manyan Hafsoshin Tsaro, an cimma matsayar tura karin dakaru 6,000 zuwa jihar don karfafa kokarin da jami’an tsaro ke yi a yanzu; Nan ba da dadewa ba sojojin za su isa jihar domin fara ayyukansu,” a cewarsu.

Ya ce “Shugaban Kasa ya amince da wa’adin da ’yan bindiga za su amince da yarjejeniyar sulhun namu, su mika makamansu ga gwamnati.”

Domin, “Duk da kwanciyar hankali da shirin tattaunawa da sulhun ya kawo, yawancin ’yan bindigar sun ki shiga, sun zabi ci gaba da kai hare-hare da sauran munanan ayyukannsu.”

Da yake sanar da matakan tabbatar da tsaron da Gwamnatin Jihar ta dauka, Matawalle ya ce, “Gwamnati ta lura da cewa akwai masu zagon kasa da marasa kishi a ciki da wajen jihar da ke ba da bayanai gare su da ba a kai ga ganowa ba.”

Ya gargadi ’yan siyasa kan yin zagon kasa ga tsaron jihar sannan ya umarci sarakunan gargajiya da Shugaba kananan hukumomi da cewa “koyaushe su ci gaba da kasancewa a yankunansu don lura da shigowar wasu halayyar da ba a yarda da su ba.

“An hana daukar mutum sama da biyu a kan babur nan take, an umarci jami’an tsaro su kamo masu karya wannan umarnin don gurfanar da su a gaban kotu,” inji shi.

Kazalika an dakatar da zirga-zirgar babura cikin ayari a Zamfara.

Masu amfani da shafukan sada zumunta kuma su daina yada labaran karya, saboda gwamnati “ba za ta sake lamuntar irin wannan rashin da’a ba kuma za ta yi ladabtar da duk wanda aka samu da wannan aikin”.

Bayanan nasa na zuwa na sa’o’i kadan bayan ganawa da ta tu da Manyan Hafsoshin Tsaro da suka ziyarci Jihar inda suka tattauna da kwamandojin soji da sarakunan gargajiya a Gusau kan hanyoyin kawo karshen matsalar a ranar Talata.

Kimanin mako biyu kuma ke nan bayan ’yan bindiga sun sace dalibai mata 279 da shekarunsu ba su wuce 16 ba a makarantar sakandaren kwana ta GGSS Jangebe, a Karamar Hukumar Talata Mafara.

Garkuwa da Daliban Jangebe da aka sako bayan kwana biyar ya sa Gwamnatin Zamfara rufe makarantun kwana.

Shugaba Buhari ya haramta tashin jirage da ayyukan hakar ma’adinai a Jihar tare da alkawarin sace ’yan daliban shi ne zai zama na karshe.