✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Matata da ’ya’yana suna haduwa su lakada min duka’

Magidancin ya nemi kotu ta raba aurensa da matarsa, saboda ita da ’ya’yansu na yawan lakada mishi duka

Wani tsohon ma’aikacin banki ya nemi kotu ta raba aurensa da matarsa, kan yadda ita da ’ya’yansu suke yawan lakada mishi duka.

Dattijon  mai shekara 62 ya shaida wa Kotun Gargajiya da ke Legas cewa matar tasa tana yawan lakada mishi duka.

“Matasa tana lakada min duka kuma tana tunzura ’ya’yanmu hudu su dake ni; Babban dana na barazanar ba ni guba.

“Na uku kuma ya yi barazanar caka min wuka, kullum suna hada baki a kaina,” inji shi.

Amma matar, mai shekara 58 ta musanta zargin, tana mai shaida wa kotun cewa mijin nata ne ba ya faranta mishi rai.

“’Ya’yanmu sun taso ne suna ganin yadda yake duka na, sai suka kare ni, amma ba su taba dukan shi ba,” a cewarsa.

Shugaban kotun, Saadat Quadri, ya caccaki yaran kan zargin da mahaifin nasu ya yi,sannan ya dage sauraron shari’ar zuwa 26 ga watan Mayu.