✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya yi wa matar wansa fyade ya kashe ta a Binuwe

An tsinci gawarta a gona da alamar an yi mata fyade kuma an sassare ta da adda a hancinta da kanta.

Jama’ar gari sun kona wani matashi da ransa kan yi wa matar dan uwansa fyade sannan ya kashe ta a kauyen Achoho da ke Karamar Hukumar Gwer ta Gabas a Jihar Binuwe.

Ranar Litinin jama’a suka cafke matashin mai shekaru 22 suka banka masa wuta ya mutu, saboda ya kashe matar dan uwan nasa bayan ya yi mata fyade a gona.

Shaidu sun ce ranar Juma’a matashin suka je gona tare da matar dan uwan nasa, amma dukkansu ba su dawo ba, sai daga baya aka tsinci gawarta a gonar da alamar an yi mata fyade kuma an sassare ta da adda a hancinta da kanta.

Daga bisani shi kuma aka samu labarin yana garin Tse-Agberagba, hedikwatar Karamar Hukumar Konshisha LGA, inda mahaifiyarsa take aure, amma da aka je can ba a same shi ba.

A hanyar dawowa daga inda mahaifiyarsa take ne masu neman sa suka yi kicibus da shi a kauyen Agidi, suka far masa da duka.

A cewarsu, matashin ya amsa cewa ya yi wa matar dan uwan nasa fyade sannan ya kashe ta, kafin su cinna masa wuta su kona shi.

Kakakin ’yan sandan jihar Binuwe, SP Catherine Anene, ba ta sa kiran waya da rubutaccen sakon wakiliyarmu na neman karin bayani kan lamarin ba.