Wani matashi ɗan shekara 32 ya maƙure mahaifinsa mai shekaru 68 har lahira saboda sayen babur.
Matashin ya yi wa mahaifin nasa wannan aika-aika ne saboda ya nemi dattijon ya saya masa sabon babur amma ya ƙi.
Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Abdulateef Suleiman, ya shaida wa kotu ranar Juma’a cewa matashin ya kashe mahaifinsa ne a yankin Isua Akoko da ke Ƙaramar Hukumar Akoko ta Kudu maso Gabas na Jihar Ondo.
Ya ƙara da cewa ’yan sanda sun gano cewa bayan mahaifin ya ƙi sayen babur ɗin ne aka samu rashin jituwa tsakanimsu, “a garin haka matashin ya maƙure wuyan dattijon, ya yi ajalinsa.
“Duk ƙoƙarin mahaifiyar wanda ake zargin na ceton mamacin ya faskara, saboda matashin a cikin magagin miyagun ƙwayoyi yake.”
Bayan sauraron jawaban, sai Alƙali Funke Akinboboye, ta ba da umarnin tsare matashin a gidan yari, sai ta ji daga ofishin Daraktan Gurfanarwa na Gwamnati
Daga nan ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga watan 2025.