✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya kashe yara 9 don yin tsafi a Taraba

Sai dai ikirarin wanda ake zargin ya tunzura matasa da ’yan uwan yaran da ya kashe

A Jihar Taraba, ana zargin wani matashi mai kimanin shekara 30 da hallaka yara tara ta hanyar yin tsafi.

Matashin, mai suna Mubarak Lamu, dan asalin garin Mutumbiyu ne, hedkwatar Karamar Hukumar Gassol da ke Jihar ta Taraba.

Ya tabbatar hallaka yaran ne a lokacin da ya nuna wa jami’an ’yan sanda wani rami inda ya birne su a kusa da kogin da ake kira Dan Kuturu da ke garin na Mutumbiyu.

Sai dai ikirarin na Mubarak ya tunzura matasa da ’yan uwan yaran da ya kashe, inda suka yi yunkurin kona gidan mahaifinsa, in ban da manyan garin sun lallashi fusatattun matasan sun hakura da yunkurin.

Matasan garin na Mutumbiyu dai sun yi barazanar daukar doka a hannunsu, muddin hukuma ta ki hukunta Mubarak.

Kakakin Rundunan ’Yan Sanda na Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya shaida wa wakilinmu cewa yana jiran cikakken bayanai kan lamarin daga Baturen ’Yan Sanda (DPO) mai kula da shiyyar ta Mutumbiyu.