✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya kashe mahaifiyarsa saboda wayar salula

Mahaifiyar Deepak ta hana shi kudin wayar salula.

Wani matashi dan shekara 26 mai suna Deepak ya kashe mahafiyarsa saboda ta ki siya masa wayar salula a Jihar Karnataka da ke Kudu maso Yammacin Indiya.

Tuni dai ’yan sanda suka cafke matashin wanda a cewarsu ya shiga hannu a ranar 3 ga watan Yuni, bayan an zarge shi da shake mahaifiyarsa Fathima Mary mai shekaru 50 a duniya har lahira a ranar 1 ga watan Yuni.

’Yar uwar matashin da ake tuhuma, Joyce Mary ta shigar da kara ofishin ’yan sandan cewa wasu bata gari ne suka kashe mahaifiyarsu a gonar lambunsu mai tazarar kilomita 5 kacal daga gidansu.

A cewar jami’ai, yayin da Fathima ke fita zuwa gona da safe, ta tunatar da Joyce cewa ta tura danta Deepak zuwa gona idan ya farka daga barci.

Wajen azahar Deepak yaje ya dauko mahaifiyarsa, amma bayan wani lokaci ya dawo yace bai sameta a ko ina ba.

Yayin da ’yan uwa ke neman Fathima, Joyce ta samu kira daga wayar mahaifiyarta da misalin karfe 2 na rana.

Deepak da ke gefe ya shaida mata cewa mahaifiyarsu ta fadi a gefen titin, kuma ya yi zargin cewa wani ne ya shake ta.

‘Yan sandan sun ce Deepak da isa gonar ya bukaci kudin India rupee 20,000 daga wurin mahaifiyarsa Fathima domin ya siyan wayar salula, amma ta ki ba shi kudin.

Daga nan ya daka mata tsawa bayan ta mishi gorin cewa ba su biya mata bukata, don haka ba za ta iya bashi kudi don ya sayi waya ba.

Daga nan ne Deepak ya shake mahaifiyarsa har lahira sannan ya tsere da kudi rupee 700 da ke cikin jakar mahaifiyarsa Fathima.

Lokacin da ya isa gida, ya yi kamar bai san komai ba game da ita, in ji ’yan sanda.

Daga baya, lokacin da aka tambaye shi, Deepak ya amsa laifin kamar yadda jaridar the Indian Express ta ruwaito.