✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya kashe mahaifinsa da tabarya saboda mafarki a Kaduna

Wani matashi dan shekaru 20 ya fada hannun ’yan sanda bayan ya kashe mahaifinsa a bisa zargin mahaifin da neman kashe shi a cikin mafarki

Wani matashi dan shekaru 20 da haihuwa ya fada hannun ’yan sanda bayan ya kashe mahaifinsa a bisa zargin wai yana zuwa masa a mafarki zai kashe shi.

A cewar matashin mazaunin kauyen Madakiya da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf, ya ga mahaifinsa ne a cikin mafarki kamar tsunsu amma da fuskar mutum yana kokarin kashe shi.

“Da na gan shi a cikin mafarki yana bi na da gudu, ni kuma ina ta gudu ina ihu kar ya kama ni, shi ne bayan na farka sai na dauki tabarya na buga masa yana barci” inji shi.

Anna ya shaida wa ’yan jarida cewa ya yi nadamar abin da ya aikata.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, ASP Mansir Hassan, wanda ya yagabatar da matashin ga manema labarai, ya ce tunda ya amsa lafinsa, da zarar sun kammala bincike za su aika da shi kotu domin ya fuskanci hukunci.

%d bloggers like this: