✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya daba wa matar wansa mai juna biyu wuka a Kano

Ya ciro wuka ya soka mata a ciki da wasu sassan jikinta.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta dakume wani matashi mai shekara 15 bisa zargin daba wa matar wansa mai juna biyu wuka a ciki.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa yana cewa sun samu rahoton aukuwar lamarin ne da misalin karfe 11.00 na daren ranar Alhamis da ta gabata.

DSP Kiyawa ya ce ana zargin matashin da daba wa Habiba Isa mai dauke da cikin wata takwas wuka a cikin nata.

“Nan da nan aka kai ta Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano inda aka kwantar da ita kuma daga baya aka tabbatar da mutuwar dan da ke cikinta.

“Matashin ya kai ziyara gidan dan uwan nasa ne kuma ya bukaci ganin matar.

“Da ya fuskanci ta tsorata kuma tana kokarin kiran mijinta a waya sai ya dauki tabarya ya karbe wayar sannan ya ciro wuka ya soka mata a ciki da wasu sassan jikinta,” a cewar Kiyawa.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis da ta gabata ce aka zargi wata malamar makaranta da yi wa dalibinta dukan da ya yi ajalinsa a Unguwar Kurna da ke Jihar Kano.