Wani matashi dan shekara 22, Abdullahi Musa ya kashe kansa ta hanyar rataya a unguwar Aboro ta Karamar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna.
An tsinci gawar matashin ne rataye a jikin turakun wutar lantarki da sanyin safiyar ranar Juma’a.
- Sun da Xu: Ma’aurata mafi ya tsawo a duniya
- An kama ’yan sandan da suka yi wa budurwa kwace
- Limaman Kirista sun yaba da wa’azin Sheikh Gumi ga Fulani
Da yake zanta wa da Aminiya dangane da lamarin, Kansilan unguwar Aboro, Mallam Dahiru Yunusa Aboro, ya ce masu wucewa ne kwatsam suka yi kicibus da gawar matashin rataye a jikin turakun wutar lantarki da safiyar ranar Juma’a.
Kansilan ya kadu da yadda matashin ya yanke shawarar kashe kansa a yayin da wadanda suka san shi suka bayar da kyakkyawar shaidar cewa mutum ne nagari.
Shugaban Karamar Hukumar Sanga, Mista Charles Danladi, ya tabbatar da ingancin rahoton faruwar mummunan lamarin yayin da wakilinmu ya nemi jin ta bakinsa.
Shugaban Karamar Hukumar ya janjanta wa ’yan uwan matashin tare da neman su dauki dangana.
Sai dai Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige bai amsa kiran wayarsa yayin da ake nemi karin bayani daga bangarensa.
Ana zargin Abdullahi ya debe wa kansa tsammani ne a ranar Alhamis da daddare inda ya kashe kansa ta hanyar rataya.