✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matasan Kwango 2,000 sun nuna sha’awar shiga soja don yakar ’yan tawaye

Matasan dai na son shiga soja ne don su yaki 'yan tawaye

Rundunar sojin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango, ta ce sama da matasa 2,000 ne suka gabatar da kansu domin samun horon aikin soji da kuma kaddamar da farmaki don sake kwato yankuna da dama da mayakan M23 suka mamaye a yankin Gabashin kasar kusa da iyaka da Rwanda.

Kakakin Rundunar Sojin kasar Manjo Janar Sylbain Ekenge, ya ce yanzu haka suna ci gaba da tsara sababbin dubaru don sake kwato yankunan da ’yan tawayen suka mamaye bayan sun samu taimkon Rwanda.

Janar Ekenge ya ce, tuni aka fara daukar matasan domin yin aiki a karkashin rundunar sojin kasar, kuma kawo yanzu a yankin Goma kawai an samu sama da matasa 2,000 da suka karbi wannan kira.

Ya kara da cewa wasu matasan da tuni suka isa cibiyar bayar da horon da ke garin Kisona sun yi haka ne bisa fahimtar cewa kasar na fuskantar gagarumar barazana.