Wasu matasan Kiristoci a Jihar Filato sun hada kudi domin saya wa Masallacin Juma’ar garinsu janereta domin amfani da shi wajen kiran Sallah da kuma wa’azi a cikin watan Ramadana.
Gidan Rediyon Unity FM da ke Jos ya ruwaito cewar lamarin ya faru ne a kauyen Gana Ropp da ke Karamar Hukumar Barikin Ladi, daya daga cikin yankunan da aka yi ta fama da matsalar tsaro wanda ke kai ga rasa rayuka tsakanin Fulani makiyaya da ’yan kabilar Birom.
Wannan aiki na matasa ya gamu da yabo daga ciki da wajen Jihar Filato musamman a daidai lokacin da gwamnatin Jihar ke ta kokarin ganin ta tabbatar da zaman lafiya da kuma hada kan jama’a domin samun ci gaba.
Jihar Filato ta yi fama da rikicin kabilanci da addini tun daga shekarar 2001, abinda ya yi sanadiyar rasa dimbin rayukan jama’a da kuma asarar dukiyoyi, yayin da rashin yarda ya fadada tsakanin al’ummar jihar.
Wannan ya sa shugaban kasa na wancan lokaci Olusegun Obasanjo kafa dokar ta baci da dakatar da Gwamnan Jihar Joshua Dariye na wani lokaci, yayin da ya nada Janar Chris Muhammed Ali a matsayin Kantoma na wani lokaci.
Har ya zuwa wannan lokaci akan samu hare hare jifa jifa wadanda ke kaiga rasa rayukan jama’a da kuma asarar dukiyoyi a wasu sassan Jihar, duk da kokarin da gwamnatin Simon Lalong ke yi na wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin jihar