Wasu fusatattun matasa sun kone Makarantar Noble Kids Academy da ke Jihar Kano biyo bayan sacewa da kuma kashe yarinyar nan mai shekaru biyar, Hanifa Abubakar da malaminsu ya yi.
Aminiya ta ruwaito cewa, mamallakin makarantar, Abdulmalik Tanko da ya yi garkuwa da ita, ya kuma kashe ta, tuni ya shiga hannu inda bincike a kan lamarin ya kankama.
- Zalunci ne Arewa ta ci gaba da mulki a 2023 —Tanko Yakasai
- Gwamnatin Kano za ta fara mayar da mabarata jihohinsu na asali
Wani bidiyo da wakilinmu ya nado ya nuna yadda aka cinna wa makarantar wuta da misalin karfe 1 na daren Lahadi wayewar garin Litinin.
Tuni dai gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ba da umarnin rufe makarantar da Hanifa ta ke zuwa kafin gamuwa da ajalinta, inda kuma malamin ya binne ta kafin hukuma ta tono gawarta.
A yayin da dubban mutane ke ta tofin Allah-tsine da bayyana takaicinsu kan wannan lamari, shi ma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin cewa a tabbatar an yi adalci wajen neman hakkin yarinyar da aka kashe bata ji ba bata gani ba.
Kasa da mako guda ke nan bayan kama malamin da kuma tono gawar Hanifa, matasa suka huce fushin kisanta wajen cinna wa makarantar wuta, duk da yake wasu bayanai sun ce hayar ginin mai makarantar, Abdulmalik Tanko ya ke yi.