✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi jana’izar matar Sarkin Katsina, marigayi Alhaji Kabir Usman

Marigayiyar ita ce matar mahaifin Sarkin Katsina na yanzu.

An yi jana’izar Hajiya Hajiya Rakiyat, matar Sarkin Katsina, marigayi Alhaji Kabir Usaman.

Allah Ya yi wa Hajiya Rakiyat Kabir Usman rasuwa ne a ranar Lahadi da dare tana da shekara 82 a duniya.

Marigayiyar mata ce ga mahaifin Sarkin Katsina mai ci, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, kuma ta rasu ta bar ’ya’ya takwas.

Majalisar Masarautar Katsina ta sanar cewa an sallaci marigayiyar a safiyar Litinin a Fadar Sarkin Katsina.

Sanarwar rasuwar da mai magana da yawunta, Mallam Ibrahim Bindawa ya fitar ta ce, Sarkin Daura, Alhaji Faruq Umar, da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, da wasu manyan jami’an gwamnati na daga cikin mahalarta jana’izar.