✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babbar Sallah: Masarautar Katsina ta soke Hawan Daushe

Masarautar ta dauki wannan mataki ne saboda matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

Masarautar Katsina ta ba da sanarwar soke hawan daushe yayin bikin Babbar Sallah mai mai zuwa da za a gudanar.

Dakatarwar na kunshe ne cikin sanarwar da masarautar ta fitar a ranar Talata ta hannun Sakatarenta, Alhaji Sule Mamman-Dee.

Masarautar ta ce, ta dauki wannan mataki ne saboda matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

A cewar Mamman-Dee, Mai Martaba Sarki Abdulmumini Kabir-Usman ya yi matukar damuwa kan matsalar tsaron da ake fuskanta a wasu sassan masarautar, don haka ya ce bana baya ga sallar Idi ba zai yi wani hawa ba kamar yadda aka saba.

Mamman-Dee ya kuma ce Sarkin ya shawarci Musulmi da su ci gaba da yi wa jihar da ma kasa baki daya addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya.

A wata sanarwar mai nasaba da wannan, ita ma Masarautar Daura a Jihar Katsinan ta sanar da soke Hawan Sallah yayin bikin Babbar Sallah na bana, kamar dai yadda kakakin masarautar, Alhaji Usman Ibrahim ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai.

Ibrahim ya ce Sarkin Daura, Alhaji FarukUmar-Faruk ya umarci daukacin Hakimai da ke karkashin masarautar da kowa ya yi sallar Idi a yankinsa.

Kazalika, ya ce basaraken ya bukaci maniyyata Hajjin bana daga jihar da su sanya jihar da kasa baki daya a cikin addu’o’insu yayin gabatar da Hajji don samun zaman lafiya.

(NAN)