Shugaban Kungiyar Manoman Masara ta Najeriya, Alhaji Bello Abubakar, ya ce Najeriya ta samar da akalla tan miliyan 20 na masara a 2021.
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Jihar Katsina yayin da ya jagoranci ’ya’yan kungiyar wajen kai ziyara ga Sarkin Katsina, Dokta Abdulmumin Kabir Usman.
- NAJERIYARMU A YAU: Gaskiyar Inda Mai Mala Buni Yake A Yanzu
- Fanna Inna Abdulrahman: Shekaru fiye da 30 na shayar da ilimi
Ya ce lokacin da ya karbi shugabancin kungiyar a 2015, manoma masara na samar da tan miliyan takwas ne a shekara.
“Bayan zaba ta da aka yo a 2015, daga wancan lokaci zuwa yanzu an samu karin tan miliyan 12, wanda yanzu ya kai tan miliyan 20 gaba daya.
“Sakamakon wannan ci gaba, an samu karin noman masara a Najeriya sakamakon bullo da hanyoyin zamani ga manoma masara.
“Sun fahimci yadda ake noman masara a zamance tun daga farko har zuwa lokacin girbi,” a cewarsa.
Kazalika, ya ce akalla sama da manoman masara 500,000 ne suka amfani da tsarin tallafin Anchor Borrower na Gwamnatin Tarayya, kuma akalla mutum 80,000 ne daga Katsina suka amfani da shirin.
Shugaban ya nemi goyon bayan Sarkin kan yadda manoma za su ci gajiyar shirin tun daga kasa.
A nasa jawabin, Sarkin na Katsina ya jinjina wa shugabancin kungiyar, inda ya hore su da kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen cimma bukatar kansu.
A cewarsa, idan har suka bari ’yan siyasa suka shiga cikin tsarin ba lallai manoman da ya kamata su ci gajiyar shirin su samu damar cin moriyarsa ba.
“Matsalar tsaro ta zama babbar kalubale ga harkar noma, amma dole ne sai mun ci abinci. Don haka dole mu yi aiki tukuru,” a cewar sarkin.