✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi jana’izar kanin Sarkin Katsina

Sarkin Dawakin Tsakar Gidan Katsina Alhaji Hassan Kabir Usman yana da shekaru 55

Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya rasa kaninsa, Alhaji Hassan Kabir Usman.

Marigayi Alhaji Hassan Kabir Usman shi ke rike da sarautar Sarkin Dawakin Tsakar Gida.

Mamacin ya koma ga mahaliccinsa yana da shekaru 55  a ranar Litinin, kuma an gudanar da jana’izarsa bisa tsarin addinin Musuluncin.

An kai shi makwacinsa da ke Makbartar Dantakun bayan Babban Limamin Katinsa, Sheikh Gambo Mustapha, ya jagoranci Sallar Janai’zar.

Gwamna Umar Dikko Radda da mataimakinsa, Faruk Lawal Jobe, da sauran manyan jami’an gwamnatin jihar na daga cikin fitattun mahlarta sallar jana’izar da kuma ta’zaiyya.