✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karfe 11 za a yi Jana’izar Sarkin Dawakin Tsakar Gidan Zazzau

Da misalin karfe 11 na safiyar Litinin za a yi jana'izar Sarkin Dawakin Tsakar Gidan Zazzau, Malam Ibrahim Shehu Idris

Allah Ya yi wa Sarkin Tsakar Gidan Masarautar Zazzaun Mallam Ibrahim Shehu Idris, rasuwa.

Ana sa ran gudanar da sallar jana’izarsa a Fadar Sarkin Zazzau da misalin karfe 11 na safiyar Litinin.

Masarautar Zazzau ta sanar da cewa Sarkin Dawakin Tsakar Gida ya rasu ne a ranar Lahadi, sakamakon gajeruwar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello.

Marigayi Sarkin Tsakar Gidan Masarautar Zazzaun Mallam Ibrahim da ne ga Sarkin Zazzau, Marigayi Alhaji Dokta Shehu Idris.

Rasuwar tasa ta auku ne kwana 12 bayan rasuwar wansa, Dan Isan Zazzau, Marigayi Alhaji Umar Shehu Idris.

A yammacin ranar Talata 8 ga watan nan na Oktoba da muke ciki, Alhaji Umaru Shehu Idris ya rasu.

Bayan rasuwar ce Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya nada jikan gidan, Alhaji Mustaph Aliyu Shehu Idris a matsayin Dan-Isan Zazzau.