Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya jadadda aniyarsa ta bude dukkan iyakokin Najeriya da ke rufe muddin aka zabe shi a 2023.
Atiku, ya bayyana hakan ne ga dubban magoya bayansa a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Jihar Katsina.
- Saudiyya ta maido wa Najeriya kudin abincin alhazai N107m
- DAGA LARABA: Yadda Ake Aure Da Ciki A Najeriya
A cewar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, “Yana daga cikin alkawuran da muka dauka na dawo da tsaro da tattalin arziki. Don haka zamu bude dukkanin iyakokin Najeriya da aka rufe.
“Idan kuka ba ni dama ba zan zama irin wanda zai sa a ci gaba harbin ’yan kasuwa saboda sun dauko buhun shinkafa ba,” cewar Atiku.
Dan takarar ya kuma ce dukkanin ababen more rayuwa da ci gaba da gwamnatin PDP ta baya ta gina a jihar, an salwantar da su.
Kazalika, dan takarar ya ba da kyautar Naira miliyan 50 ga jama’ar da matsalar rashin tsaro ta shafa a jihar.
Ya bayar da kyautar kudin ne a fadar mai martaba Sarkin Katsina, Dokta Abdulmuminu Kabir Usman.
Atiku ya ce ya ziyarci Sarkin ne don neman tabarraki da shawara daga wajen shi.
Idan ba a manta, ba Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari, ta bayar da umarnin garkame dukkanin iyakokin Najeriya, saboda inganta tsaro da kuma bunkasa amfani da kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida.