✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Liman ta kashe dan kishiyarta da bugu

Ana zargin daya daga cikin matan Limamin Juma’a na Hayin Dogo a Samaru Liman Umar Sambo da kashe dan kishiyarta ta hanyar bugunsa.Matar mai suna…

Ana zargin daya daga cikin matan Limamin Juma’a na Hayin Dogo a Samaru Liman Umar Sambo da kashe dan kishiyarta ta hanyar bugunsa.
Matar mai suna Misiliha Muhammad ana zarginta ne da kashe dan kishiyarta mai suna Ahmad Umar mai kimanin shekara tara ta hanyar yi masa  mummunan duka.
Mahaifiyar marigayin Malama Hauwa Umar da wadda ake zargin dukkansu suna zaune ne a Layin Makabarta da ke Hayin Dogo, Samaru a karamar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna.
Ta shaida wa Aminiya cewa, “A ranar Asabar da ta gabata ina kwance a daki ba ni da lafiya, sai ga dana marigayi Ahmad ya zo a guje jikinsa na rawa ya ce don Allah Mama boye ni Mama Misiliha ce ta bubbuge ni da sanda ta kuma ce a kamo ni.”
Ta kara da cewa, “Ashe dama amaryanmu mai suna Amina ta aike shi ya kai mata nika jin haka sai ita ma ta fito ta ce Ahmad me ya faru Allah Ya sa dai ba ka zubar da nikan da na aike ka ba. Sai ya ce a’a ai Mama Misiliha ce ta biyo ni tana duka bayan na dawo daga kai miki nika.”
Mahaifiyar ta ce to tunda Ahmad ya kwanta ya ce kansa na ciwo yana ta rawar dari ba su gane masa ba, sai ita da amaryarsu hankalinsu bai kwanta ba ganin halin da yake ciki sai suka dauke shi zuwa wani asibiti da ke kusa da mu mai suna SAbANNA POLYCLINIC a Hayin Dogo, Samaru. “Da zuwanmu sai mahaifinsa Liman Umar Sambo wato mai gidanmu ya same mu a asibitin, bayan likitoci sun duba shi sai suka ce hadari ne ko bugewa ne ya yi? Sai na ce musu a’a duka ne kishiyata ta yi masa, sai suka ce za su sanya masa abin da ke taimaka wa mutum domin yin numfashi, kuma suka sanya masa wata na’ura da ke janyo jini daga cikin cikinsa tana fitowa da shi waje,” inji ta.
Ta ce kafin nan da mijinsu ya zo sai ya ce karya ne ai dama dansa Ahmad yana da ciwon sikila dama bai cika lafiya sosai ba, “Ni kuma na ce a’a dana ba ya da cutar sikila domin yau shekararsa tara ban taba kai shi asibiti da sunan sikila ba, kuma idan sikila ne wane asibiti ake kai shi, kuma wane likita ke duba shi tsawon shekara tara da ya yi a raye?”
Ta ce jayayyar da suka yi ta nuna mijinsu yana goyon bayan kishiyar tata sai su kuma likitocin suka ce sai an kira ’yan sanda sun zo, in ba haka ba, ba za su ci gaba da duba yaron ba. “Nan da nan muka sanar da ofishin ’yan sanda na Samaru suka zo suka yi binciken da za su yi, sakamakon binciken da likitoci suka yi ne ya sa aka kama kishiyar.
Malama Hauwa’u Umar ta ce ta ji mamaki da ta samu labarin cewa daga baya ’yan sanda sun ba da belin kishiyarta da take zargi da kashe mata da.
Malama Hauwa’u ta ce sun dade suna shan wahalar kishiyar tata ita da ’ya’yanta da abokan zamanta har ma da makwabta, “Ka ga wannan konewar da kake gani a kafata ita ce ta juye min talge a kafa wata shida da suka wuce, ganin yadda mijinmu Liman ke daure mata gindi dama ta sha alwashin cewa sai ta ga bayana da ’ya’yana. Kuma ita ta yi sanadiyar da Liman ya kori uwar gidanmu mai suna Ramatu. To wai sai na ji an ce an ba da belinta wannan abu bai min dadi ba don haka nake rokon duk wanda yake da iko ko masu kare hakkin al’umma, su zo su bincika su kwato mana hakkinmu saboda mu masu rauni ne,” inji ta.
Ita ma amaryarta Amina Mu’azu ta ce, irin halin da suka samu kansu a ciki game da abokiyar zamansu abin ba dadi kuma mai gidansu duk da kasancewarsa malami kuma jagora amma abin ya fi karfin sa domin sai abin da Misiliha ta ga dama take yi.
Wasu makwabta da ba su so a fadi sunayensu sun ce irin halin da Liman ya tsinci kansa a ciki dangane da wannan matar tasa abin ba dadi sai dai a ce jarrabawa ce domin kuwa aurenta tara shi ne mijinta na goma.
Aminiya ta garzaya ofishin ’yan sanda domin jin ta bakinsu a kan ba da belin Misiliha, mataimakiya a ofishin ta ce kwanan Misiliha uku a hannunsu kuma ba su ba da belinta ba sai bisa shawarar jami’an kiwon lafiya domin ita Misiliha tana dauke da tsohon ciki kuma ta fara nuna alamun haihuwa don haka suka ba da belinta a bisa sharudda kuma gawar yaron na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya da zarar sun kammala bincike za su tura su Kaduna.
A gidan su Misiliha da ke Unguwar ’Yar dorawa, Layin Maibulala gidan danda Hayin Dogo Samaru, Misiliha ta ce, wannan zargi ba gaskiya ba ne sharri ne kawai mutane suke yi mata. Ta ce “Batun dukan yaro da aka ce na yi eh na buge shi, amma ba irin bugun da ake zargin na yi ba, domin na kira shi zan aike shi sai kawai ya zage ni don haka na kama shi na buge shi ya gudu na ce a kamo shi. Batun kona kishiyata kuma ba da gangan na yi ba, na zo kama yaro ne don ya yi min laifi shi ne ya boye a wurinta sai talgen ya zube mata a kafarta.”
Wakilinmu ya yi kokarin ganawa da Liman Sambo Limamin Juma’a na Hayin Dogo amma abin ya ci tura.
Wakilinmu ya buga wa kakakin rundunar ’yan sanda na Jihar Kaduna Abubakar Zubairu waya har sau biyar bai dauki ba, kuma ya aika masa da sako kan lamarin bai ba shi amsa ba.