Hajiya Ladi Audu Bako, matar Gwamnan Jihar Kano na farko, Audu Bako ta rasu
Ta rasu ne a ranar Laraba tana da shekara 93 bayan ta sha fama da rashin lafiya a asibitin ‘Prime Specialist’ da ke Kano.
- Gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar hana fita a wasu yankunan Jihar
- Kotu ta saki Donald Trump bayan musanta zargin da ake masa
Aminiya ta tattaro cewa za a yi jana’izarta a Masallacin Malam Inuwa Dutse da ke unguwar Sallari bayan Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da misalin karfe 1:30 na rana.
Audu Bako dan sandan Najeriya ne kuma gwamnan Jihar Kano na farko a lokacin mulkin soja na Janar Yakubu Gowon bayan an kafa jihar daga yankin Arewa.