Shakira, matar dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen Gerard Pikue ta sake haihuwar da namiji a ranar Juma’ar da ta gabata.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta Mirror ta kalato, matar ’yar kimanin shekara 37, kuma shahararriyar mawakiya, a yanzu ta haifi danta na biyu ne bayan wanda ta haifa kimanin shekara 2 da suka wuce.
Matar ta haihu ne a asibitin da ta haifi danta na farko mai suna Milan, a asibitin da take ziyarta don yin awon ciki. Kuma a asibitin ne ta haifi danta na farko mai suna Milan.
Tuni Lionel Messi daya daga cikin takwarorin Pikue a kulob din Barcelona ya aika wa matar da kuma mijin nata sakon taya murna a kan karuwar da suka samu.