Likitoci sun cika da mamaki bayan wata matar aure da ta je ganin likita ta shaida musu cewa ta shafe sama da shekara 40 rabonta da yin barci.
Matar mai suna Li Zhangyinh, da ke Lardin Henan da ke Gabashin kasar China, ta shaida wa kafafen yada labaran kasar cewa rabonta da ta runtsa idununta da sunan ta yi barci tun tana ’yar shekara biyar.
- An kama uwa tana lalata da dan cikinta a gona
- Ranar 9/11: Shugaban Al-Ka’ida ya fitar da sabon bidiyo
Mijin Misis Li da makwatanta sun tabbatar wa kafafen yada labaran kasar cewa su ganau ne cewa a tsawon shekarun da suka yi da ita ba ta barci.
– Da gaske ne
Makwabtanta sun shaida wa ’yan jarida cewa sun tabbatar da gaskiyar ikirarin Misis Li cewa ba ta yin barci, saboda sun yi duk abin da za su iya domin ganin kwakwaf, kuma sun tabbatar da gaskiyarta.
Sun ce sai da ta kai suna tsara wa kansun yadda za su rika yin karba-karba a tsakaninsu, domin lura da Misis Li, ba dare, ba rana, amma ba su taba ganin ta yi barci ba, karshenta ma dai sai dai wasunsu su yi barci.
Mijin Misis Li, mai suna Liu Suoquin, ya ce tun da ya aure ta bai taba ganin ta yi barci ba, kodayaushe idanunta kuri suke — hasali ma tana kwana ne tana aikace-aikacen gida saboda ba ta iya barci.
Mista Liu ya ce da farko ya dauka barci ne kawai matar tasa ba ta ji ko kuma cutar rashin barci na Insomnia ke damun ta.
Saboda haka ya yi ta kokarin sayo mata magunguna da ke sanya barci, amma ba ta taba yin barci ba — ko da yaushe kuri take, idanunta biyu.
Li, wadda yanayin nata na rashin barci ya sa mutane ke rububin zuwa ganin ta, ta yi ta zuwa asibiti, amma likitoci sun kasa gano hakikanin matsalarta ballantana a magance ta.
Hakan ne ya sa a baya-bayan nan ta ziyarci wata cibiyar barci a birnin Beijing, inda ta bayyana wa cibiyar halin da take ciki domin a nema mata mafita.
– Bakuwar barci
Bayan nan ne tawagar wasu kwararrun likitoci suka gudanar wa bincike, daga karshe suka ce sun gano cewa a hakikanin gaskiya Misis Li tana barci, sai dai barcin nata ba kamar na sauran mutane ba ne.
Likitocin sun tabbatar cewa Li tana barci ne idan ta dan lumshe idanu ta yadda idanunta za su dan yi kasa-kasa; Amma kuma duk da haka tana yin magana.
Sakamakon gwajin da na’urar auna tafiyar kwakwalwa ya nuna lumshe idanun na Li ba ya wuce minti 10 a rana.
Sun kamanta yanayin Li da yanayi da na wasu daidaikum mutane da ke iya yin barci a yayin da suke tafiya.