Wata mata mai suna Hester Ford wacce ta fi kowa tsufa a Amurka, ta rasu bayan shafe shekara 116 a doron kasa.
Bayanai sun nuna cewa Ford wacce aka haifa kafin yakin duniya a daidai lokacin da aka kirkiro abun sha na ‘ice cream da kuma lokacin aka fara aiki a mashigin ruwan Panama, ta rasu ne ranar Asabar a gidanta da ke Jihar North Carolina.
Ford ta auri John Ford tun tana ’yar shekara 14, kuma ta yi haihuwar farko tana da shekara 15 kacal a duniya.
Tun bayan rasuwar John a shekarar 1963 wanda suka shafe shekaru 45 tare Hester ba ta sauke aure ba.
A yanzu bayan rasuwarta, Ford ta bar magada 288 da suka hada da ’ya’ya 12 da jikoki 48 da tattaba kunne 125 sannan kuma da akalla ’ya’yan tattaba kunne 120.
A yayin da rahotanni suka nuna cewa babu wanda ya san hakikanin ranar da aka haife ta, amma gwajin da aka yi ya nuna cewa ita ce BaAmurkiya mafi tsufa wacce aka haifi a shekarar 1905 a gundumar Lancaster.
Wannan mata dai ta taso ne tana aiki a wata gonar auduga yayin da daga bisani ta yi aiki na shekaru da dama a matsayin mai reno kamar yadda kafofin watsa labarai na Amurkan suka nuna.
Hukumar kididdigar Amura ta ce a shekarar 2019 aka gano cewa Ford ce mafi tsufa a kasar bayan mutuwar Alielia mai shekara 114.
Wata cibiyar bincike da nazari a kan shekarun wadanda suka shafe shekaru aru-aru a ban kasa ta Gerentology Resaerch Group, ta kiyasta shekarun Ford a matsayin wacce ta shafe shekara 115 da kwanaki 245 kafin barin duniya.
A lokacin rayuwarta yayin da aka tambayeta dalilin tsawon rai da ta yi a duniya, Ford ta ce tana fara karin kumallo ne da cin ayaba duk rana sannan ta fita cikin lambu ta shaki iska gabanin ta dawo cikin gida inda take kallon hotunan danginta tana sauraron sauti kadan-kadan.