Wata mata mai suna LaRae Perkins mai shekara 40, daga birnin Kompton, a Jihar Califoniya ta kasar Amurka tana da gemu har da saje.
Matar wacce take aiki a matsayin Wakiliyar abokan ciniki, ta kasance ta na da ciwon ‘polycystic obary syndrome’ (PCOS), wanda zai iya yin tasiri a rayuwarta ta yau da kullum, a lokuta da kuma samar da babban matakin halittun da suke da dangantaka da kwayoyin halittun jini (hormones).
- Qatar 2022: Masu tsaron gidan Faransa sun kamu da rashin lafiya
- Za A Haramta TikTok A Ma’aikatun Amurka
Wannan yana nufin halayen mutum mai PCOS na iya hadawa da fitowar gashin mutum a fuska da kuma gashin jiki.
Mutane suna tambayar ta ko ita mace ce ko namiji, ko kuma a ce mata, ‘kai wanene?’
“Alamomina sun sa na ji ni ina rayuwar kadaita, ina jin kunya da samun bambancin rayuwa. Ina jin karaya da zama cikin rudani da tunani,” inji ta.
Amma yanzu, LaRae ta rungumi gashin fuskarta, kuma ta yi alkawarin ba za ta taba lalata gashin ba saboda lafiyar fatarta.
“Na fara samun alamun cutar PCOS a lokacin da na kusa balaga, a lokacin da nake shekara 12 amma ina da gashi a fuskata da nake rayuwata da shi,” inji ta.
“Abin da kawai aka ambata a lokacin shi ne cewa ina da kashi mafi girma na kwayoyin halittar maza da aka sani da ‘androgen’ fiye da yawancin mata.
“Alamomin PCOS sun hada da yanayin haila ba kowane lokaci ba – wannan shi ne yadda na fara. Dole ne aka sanya min maganin hana haihuwa don daidaita shi.
“Ina da kaurin kumatu mai saje da ke haduwa da gashin kaina tun ina karama.”
Wani bangare na dalilin da ya sa LaRae ta ji ita kadai lokacin da ta fara fuskantar alamun cutar PCOS dinta, saboda ba ta da tarihin ko iyayenta suna da kwayoyin cutar.
A halin yanzu ba ta kula da cutar PCOS.
“Ban yarda da kowane daya daga shawarwarin jiya na nau’in PCOS ba.
“Maganin cutar sun hada da cire kananan gashin, cire gashin sassan jiki da yin aski.
“Ina son fuskata da fatata sosai, don ko kuma na yi abin da zai haifar da karin al’amura ta hanyar kokarin cire wani abu wanda ba zai taba tafiya ba har abada ba, kuma ba ni da iko.”
LaRae ta samu ra’ayoyi mabanbanta daga mutane tsawon shekaru amma tana amfani da duk wata kulawar da za ta iya samu.
“Ina mai da hankali ne kawai ga abu mai kyau kuma ina amfani da mara kyau a matsayin sinadarin da zai sa na ci gaba da yin tasiri da ilmantar da mutane,” inji ta.