Sadiya Amin, matar da mijinta ya daure ta a daki tsawon watanni ta rasu a asibiti da aka kwantar da ita.
A daren Lahadi ne daya daga cikin masu jinyarta tare da taimaka mata, a karkashin Gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo Foundation, Musa Abdullahi Sufi ne ya sanar da rasuwar ta shafinsa na Facebook.
- An ceto matar da mijinta ya daure tsawon watanni
- Kotu ta raba auren matar da mijinta ya kama da kwarto
Daga bisani mahifiyarta da ta kai ziyara inda take da dawo da ita Kano, bayan ta ga halin da ta ke ciki.
Fitacceen dan gwagwarmayar ya ce ba za su kyale lamarin ba, sai sun dauki matakin da ya dace wajen bi wa marigayiyar hakkinta.
“Yanzu za mu dukufa wajen nemo wa Sadiya hakkin ta wajen wannan miji da ya zalunce ta,” in ji shi.