✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matan PDP sun yi zanga-zanga tsirara kan sakamakon zaben Gwamnan Nasarawa

Matan dai na neman INEC ta ayyana dan takararsu a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna

Wasu mata magoya baya da mambobin jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa sun gudanar da zanga-zanga a Lafiya, babban birnin Jihar suna neman a sake duba sakamakon zaben Gwamnan da ya ba APC nasara.

Sai dai daga cikin masu zanga-zangar ta ranar Litinin, har da wadanda suka fita tsirara suna rera wakoki cikin harshen Hausa, dauke da ganyakai a hannuwansu.

Aminiya ta rawaito cewa ’yan sanda a ranar Lahadi sun sanar da haramta kowacce irin zanga-zanga saboda dalilai na tsaro.

Da take yi wa manema labarai jawabi yayin zanga-zangara a sakatariyar PDP da ke Lafiya, Shugabar Matan jam’iyyar a Jihar, Stella Oboshi, ta ce dan takararsu, David Ombugadu ne ya lashe zaben.

Ta tsaya kai da fata cewa ba Gwamna mai ci, Abdullahi Sule na APC da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a bayyana ne ya lashe zaben ba.

Ta ce ’yan jam’iyyar za su ci gaba da zanga-zangar ta lumana har sai an biya musu bukatarsu.

A wani labarin kuma, jam’iyyar APC a Jihar ta bukaci ’yan jam’iyyar ta PDP da su garzaya kotu idan ba su gamsu da sakamakon zaben ba.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Douglas Otaru, ia cikin wata sanarwa ya gargadi PDP kan cin zarafin mata ta hanyar sa su zanga-zanga tsirara saboda zaben.