Wasu mata magoya baya da mambobin jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa sun gudanar da zanga-zanga a Lafiya, babban birnin Jihar suna neman a sake duba sakamakon zaben Gwamnan da ya ba APC nasara.
Sai dai daga cikin masu zanga-zangar ta ranar Litinin, har da wadanda suka fita tsirara suna rera wakoki cikin harshen Hausa, dauke da ganyakai a hannuwansu.
- Kotu ta aike da mutumin da ya sayar da mahaifinsa ga matsafa kan N1.8m kurkuku
- NAJERIYA A YAU: Matsin tattalin arziki na neman hana yin burodi – Kungiya
Aminiya ta rawaito cewa ’yan sanda a ranar Lahadi sun sanar da haramta kowacce irin zanga-zanga saboda dalilai na tsaro.
Da take yi wa manema labarai jawabi yayin zanga-zangara a sakatariyar PDP da ke Lafiya, Shugabar Matan jam’iyyar a Jihar, Stella Oboshi, ta ce dan takararsu, David Ombugadu ne ya lashe zaben.
Ta tsaya kai da fata cewa ba Gwamna mai ci, Abdullahi Sule na APC da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a bayyana ne ya lashe zaben ba.
Ta ce ’yan jam’iyyar za su ci gaba da zanga-zangar ta lumana har sai an biya musu bukatarsu.
A wani labarin kuma, jam’iyyar APC a Jihar ta bukaci ’yan jam’iyyar ta PDP da su garzaya kotu idan ba su gamsu da sakamakon zaben ba.
Mai magana da yawun jam’iyyar, Douglas Otaru, ia cikin wata sanarwa ya gargadi PDP kan cin zarafin mata ta hanyar sa su zanga-zanga tsirara saboda zaben.