Kungiyar Jarumai Mata A Masana’atar Kannywood (AKAFA) ta ziyarci Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Uztaz Haroun Muhammad Ibn Sina, a ofishinsa.
Hukumar ta bayyana ta shafinta na Facebook cewa kungiyar ta kai ziyarar ce a karkashin shugabarta, Rashida Abdullahi Mai Sa’a.
- Wasu ’yan uwa sun yi wa ’yar shekara 4 fyade
- Yajin aiki: ASUU ta caccaki dalibai kan juya mata baya
- NAJERIYA A YAU: Yadda Nada ’Yan APC Kwamishinonin INEC Zai Shafi Zaben 2023
Shugaban Hukumar kuma Babban Kwamandan Hisbah a Kano, ya bayyana farin ciki da ziyarar, duba da cewa manufofin kungiyar sun yi daidai da ayyukan hukumarsa na dakile ayyukan barna.
Hukumar ta kuma amince ta bai wa kungiyar matan na Kannywood goyon baya wajen cim-ma manufofinta na gyara a sana’arsu ta fina-finan Hausa.
A nata jawabin, Mataimakiyar Babban Kwamandar Hisbah, Ummu Kulthum Kassim, ta yaba wa kungiyar bisa shirinta na tsaftace harkar fina-finan Kannywood, da kuma yadda wasu daga cikin jaruman Kannywood mata ke kokarin kyautata mu’amalarsu da kuma kamun kai.
A jawabinsa, Mashawarcin Gwamnan Kano kan Hukumar Hisbah, Mujjitaba Baban Usama, kira ya yi ga matan da su tsarkake niyyarsu da kuma aiki don Allah.
Tun da farko, a jawabin shugabar kungiyar, Rashida Abdullahi Mai Sa’a a, ta ce sun kawo ziyara ne don gabatar da sabuwar kungiyarsu ta AKAFA da manufofinta ga hukumar, da nufin tsaftace harkar fim.
A baya dai Hukumar Hisbah ta sha kamen mata a matattarar yin badala da gantali, wadanda ta ce ’yan fim ne.