Kashi 73% na mata a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun ce daidai ne miji ya lakada wa matarsa duka.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamantin Jihar, Muhammad Abdullahi ya shaida wa taron kaddamar da Rahoton Halin da Al’ummar Duniya ke Ciki na 2021 wanda Asusun Majalisar Dinkin Duniya kan Yawan Jama’a (UNPFA) tare da hadin gwiwar wata Hukumar Tsare-tsare ta Jihar (PBC).
A cewarsa binciken ya gano kashi 38% na ’yan matan a Karamar Hukumar Soba ana aurar da su ne kafin su kai shekara 15.
Sai kuma kananan hukumomin Kubau da Kudan, inda kashi 30 da ’yan mata ana aurar da su ne kafin su kai shekara 15.
A babban hadimin gwamnatin ya ce an samo alkaluman ne ta hanyar binciken gida-gida da hukumar kidiggar jihar ta gudanar wanda a halin yanzu masu ruwa da tsaki a harkar ke kokarin tantancewa.
A cewar jami’in, binciken a matakin shiyya ya nuna kashi 32% na ’yan mata a Shiyyar Arewacin Kaduna ana aurar da su ne tun kafin su kai shekara 15 da haihuwa.
A Shiyyar Kudancin Kaduna kuma kashi 17% na ’yan mata ana musu aure ne suna kasa da shekara 15, sai Shiyyar Kaduna ta Tsakiya inda ake wa kashi 15%.
Yi wa mata kaciya
Jami’in ya kara da cewa kashi 49 cikin 100 na ’yan mata ne ake yi wa kaciya a karamar Hukumar Makarfi, sai Karamar Hukumar Giwa inda ake yi wa kashi 34 cikin 100 na ’yan matan kaciya.
Wakiliyar hukumar UNFPA a Najeriya, Ulla Muellar wadda mataimakiyarta, Erika Godson, ta wakilce ta, ta ce wannan ne karon farko da rahoton ya mayar da hankali kan abin da ya shafi ’yancin jikin dan Adam kai tsaye.
Ta ce hakan ya ya bai wa mata damar yin zabi a kan jikunansu ba tare da nuna shakkun a ci zarafinsu ko kuma wani ya yi musu zabin abin da ya shafe su.