Assalamu alaikum wa rahamatulla, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan batutuwan da za su zo cikinsa, amin.
Ga bayani kan hanyoyin da matasa masu fama da zinar hannu za su bi don rabuwa da ita. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Mataki na 1: Kyautata Niyya
Matashi ya daura niyyar yin duk abin da ya kamata don rabuwa da wannan dabi’a; ‘Dukkan ayyuka ba su tabbata sai da niyya’ kamar yadda Manzon Allah SAW ya fada mana, don haka dole a daure a daura niyya; niyya mai karfi, don in mutum bai kyautata niyyarsa ba, cikin dan kankanen lokaci da fara kokarin dainawa, zai ji ya kasa, don haka sai matashi ya tabbatar niyyarsa ta barin yin da gaske yake har cikin kashin zuciyarsa, ba wai kawai ya yi niyya da niyyar karyawa ba. Kuma ko da yaushe mutum ya ji kamar ba zai iya ba, sai ya tuna da karfin niyyarsa, da alkawarin da ya yi wa kansa, da kuma tunanin cewa raggwanci ne a gare shi a ce ya kasa cika niyyarsa. Sannan kullum ya rika yi yana kara jaddada, kaurara da karfafa niyyarsa.
Mataki na 2: Magani daga Manzon Allah SAW
1. Babban maganin da zai raba matashi da zinar hannu, shi ne yin aure kamar yadda Manzon Allah SAW ya yi umarni a cikin wani sahihin Hadisi:
“Ya ku taron samari! Duk wanda ya samu dama a cikin ku to ya yi aure domin yana tsare gannai da al’aura, wanda bai samu hali ba to sai ya yi azumi domin azumi yana dakusar sha’awa.”
2. Haka kuma Allah SWT Ya yi umarni cikin Suratur Nur, ga wanda bai sami ikon yin aure ba da ya tsare kansa har zuwa lokacin da Allah SWT Ya huwace masa. Tsarin da zai wa kansa shi ne yawan yin azumi a-kai-a-kai kamar yadda Annabi SAW Ya sanar mana.
3. Wani maganin kuma daga Annabi SAW, shi ne karanta surorin karshe na Al-kur’ani Mai Girma a tafin hannu ana shafewa sau uku, sai matashi ya karantasu yana shafewa a jikinsa duk lokacin bukatar zinar hannu ta muntsile shi, take yanke za ta sake shi cikin yardar Allah.
4. Haka kuma sai a karanta wannan addu’a ana shafawa a kan kirji daidai inda zuciya take, da kuma saman kai da gaban goshi mazaunin hankali don sanyayar da wutar sha’awa domin nan ne makunnarta:
• Bismillah-sau 3
• A’uzu bi izzatillahi wa kuduratihi min sharri ma ajidu wa uhazir-sau bakwai
Mataki na 3: Gyara zuciya
Mu sani cewa fitinar sha’awa a zuciya take, daga cikin zuciya take bijirowa, zuciya kuma nan ne masaukar rade-rade da zuge-zugen shaidan da na nafsin dan Adam; don haka mai son ya iya danne fitinar sha’awarsa duk lokacin da ta tafarfaso masa, sai ya fara da gyara zuciyarsa tukunna. To ya ake gyara zuciya? Ana gyara ta ne ta hanyar cika ta da tsarkakakku kuma kyawawan tunani da shau’uka; da yanke duk wata igiyar munanan tunani daga cikinta, da goge mazaunin duk wani mummunan shauki. Daga nan sai kyautata dabi’u da halaye da ayyuka, duk wata dabi’a, wani hali ko wani aiki da mutum ke yi indai ba mai kyau ba ne, to yin fatali da shi zai kara haskaka masa zuciyarsa. Kyawawan dabi’u sun hada da yawan murmushi, taimaka wa ‘yan uwa, makwabta da abokai, yin gaskiya da rikon amana, da sauran su. Kyawawan ayyuka sun hada da taka tsan-tsan wajen tsaida addini, duk abin da aka san ba daidai ba ne a addinance sai a yi kokari a bar shi komii dadinsa ko ribarsa.
Mataki na 4: Inganta imani
Wannan wani bangare na gyaran zuciya; domin, imani tsoron Allah da tauhidi duk a zuciya suke; don haka mai fama da wannan matsala, ya yi kokarin inganta imaninsa ta hanyar dawwamar da tsarkakakken tauhidi a zuciya; cika zuciya da tsoron da Allah SWT; Yawan tunanin Allah a zuci da waje, yin zikiri da yawan yabon Allah SWT, da yawan daukaka shi da kambama shi duk suna wanke zuciya su sa ta yi kyalli. Allah SWT Ya fada cikin Alkur’ani mai girma cewa: “Lallai da ambaton Allah ne zukata kan sami natsuwa.” Shaidan ba ya iya zama cikin zuciyar da ke ambaton Allah ballantana har ya malala cikin hanyoyin jininta, to ta yaya kuwa har zai tafarfasar da fitinar sha’awar wannan zuciya?
Haka kuma, mu sani cewa Sallolin biyar na farilla ba su isa ga mai neman kubuta daga fitinar sha’awa, dole sai an hada da nafiloli kamar wadanda ke like da sallolin farilla, sallar walha, sallar shaf’i da wutiri, raka’atainil fajri da sallar tsayuwar dare da tsawaita ruku’u da sujadun cikinsu ta hanyar karanta gaba daya addu’o’i, zikiran da ke cikinsu. Sannan sai yawan ambaton Allah kodayaushe ko da lokacin da mutum yake cikin aiwatar da wasu ayyuka ne na yau da kullum da yawaita karatun Alkur’ani Mai Girma da yawan yin azumi; wadannan duk abubuwa ne da za su kwaranyo da ruwan imani cikin zuciyar matashi, su kuma gina masa katuwar ganuwar da za ta hana makaman shaidan isa zuciyarsa ballantana har shaidan ya samu galabar tura shi ga afka wa sabon Allah Mahalicci.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba in Allah Ya kai mu, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.