Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce sabbin matakan da aka dauka sun fara tursasa ’yan bindiga a Jihar sakin wadanda suka yi garkuwa da su ta karfin tsiya.
Gwamnan, wanda ya bayyana hakan yayin wata hirarsa da Sashen Hausa na Deutche Welle a ranar Litinin ya ce hakan ya biyo bayan toshe musu hanyoyin samun abinci da man fetur da kuma na sadarwa da aka yi.
A cewarsa, mutanen da aka sace kuma suka shafe makonni ko ma watanni a hannun masu garkuwar yanzu sun fara dawowa gidajensu, su kuma ’yan bindigar na guduwa suna barin baburansu bayan man cikinsu ya kare.
Matawalle ya ce, “Babban Hafsan Sojin Kasa ya ziyarci Jiharmu don duba lamarin. Sojoji da kuma ’yan sa-kai na yankunan na can suna kokarin shiga dazuka domin zakulo ’yan bindigar.
“Kazalika, sojoji na ci gaba da kai munanan hare-hare yanzu haka. Nan ba da jimawa ba za mu tarwatsa dukkansu, muna samun gagarumar nasara.
“Babu inda zan je, zan zauna a Jihar tsawon wannan lokacin da za a dauka ana aikin. Dole nima na ji abin da kowa ya ke ji, musamman na katse hanyoyin sadarwa.
“Kamar yadda ku ke gani, mun kafa shingayen bincike a duk tsawon kilomita biyar a fadin Jihar ta yadda babu wani bata-gari da zai sha,” inji Gwamna Matawalle.
A makon da ya gabata ne dai aka sanar da kakkatse dukkan hanyoyin sadarwa a Jihar na tsawon makonni biyu domin a hana ’yan bindigar da masu hada baki da su hanyoyin tattaunawa da juna.
Gabanin haka kuma, gwamnatin Jihar ta hana sayar da man fetur a cikin jarkoki, ta rurrufe dukkan gidajen mai da kasuwanni da nufin yin kofar rago a cikin irin matakan da ake dauka wajen yaki da su.