Mataimakin Shugaban Kasar Gambiya, Badara Joof, ya rasu a kasar Indiya.
Shugaban Kasar, Adama Barrow ne ya sanar da rasuwar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter da safiyar Laraba.
- Mun kashe $1bn wajen kwato yankunan da ’yan ta’adda suka mamaye – Buhari
- DAGA LARABA: Alakar ’yan aiki da iyayen gidansu: A ina gizo ke saka?
“Ya ku ’yan uwana ’yan Gambiya, cikin yanayin jimami da alhini nake sanar muku da rasuwar Mataimakina, Mai Girma Badara Alieu Joof. Ya rasu ne a kasar Indiya bayan wata gajeruwar rashin lafiya. Allah Ya jikansa Ya ba shi aljannar Firdausi,” kamar yadda Adama Barrow ya wallafa a Twitter.
To sai dai sanarwar ba ta bayyana lokacin da ya rasu ba, da kuma ko ya je ganin likita ne kafin rasuwar tasa.
Badara Joof dai ya yi karatunsa a Jami’ar Bristol da kuma digirinsa na biyu a fannin Adabin Turanci daga Jami’ar Landan da kuma a fannin Tattalin Arziki daga Jami’ar Bath.
Ya fara aikin gwamnati ne a matsayin malamin Turanci a Kwalejin Gambiya.
A shekarar 2014, Bankin Duniya ya nada Badara a matsayin kwararren jami’in ilimi a kasar Senegal.
A ranar 22 ga watan Fabrairun 2017, Shugaba Adama Barrow ya nada marigayin a matsayin Ministan Ilimi mai Zurfi, Bincike da Kimiyya da Fasaha.