An yi jana’izar marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi, a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu, inda dubban jama’a suka halarta.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, sun halarci jana’izar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi.
- Basakkwacen da ya yi ridda ya sake karɓar addinin Musulunci
- Tinubu zai tafi ziyarar makonni biyu a Faransa
An gudanar da sallar jana’izar ne a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu, inda Farfesa Sani Zahradden ya jagoranci sallar.
Dubban jama’a ne suka halarci jansiza5 marigayin.
Har ila yau, Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, ya halarci jana’izar.
Marigayi Alhaji Abbas Sunusi, ya rasu ne a daren ranar Talata a gidansa da ke Kano bayan doguwar jinya.
Ya rasu yana da shekara 92 a duniya.
An birne shi a makabartar Gandun Albasa.
Domin nuna alhini game da rasuwar marigayin, Gwamnatin Jihar Kano da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, sun dakatar da bukukuwan Sallar da suka shirya gudanarwa a yau Laraba.
Marigayi Galadima ya riƙe mukami mafi girma a Masarautar Kano, kuma shi ne mahaifin Abdullahi Abbas, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano.
Ga hotunan yadda jana’izar ta gudana: