Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina ya ajiye mukaminsa na Kwamishinan Noma da Albarkatun Kasa domin tsayawa takarar gwamna a jihar.
Mataimakin gwamnan ya ajiye mukamin ne kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar ga masu rike da mukaman siyasa da ke son tsayawa takara.
- 2023: Sakataren Gwamnatin Katsina ya ajiye mukaminsa
- Dalilin da jirgin soja ya kashe kananan yara a Neja —Gwamnati
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da take dauke da sa hannun kakakinsa Ibrahim Musa Kallah.
Ya bayyana cewa ya rubuta takardar ajiye mukaminsa a ranar 14 ga watan Afrilu, 2022 domin bayyana kudinrinsa na tsayawa takarar gwamna a jihar ta Katsina.
Ya ce mataimakin gwamnan ya mika godiyarsa ga Allah da kuma Gwamnan Aminu Bello Masari da ya ba shi damar ba da tasa gudummuwa wajen bunkasa harkokin noma a jihar ta Katsina.
Aminiya ta ruwaito cewa Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dokta Mustapha Inuwa ya ajiye mukaminsa don tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar a zaben 2023.
Kazalika, Mai Bai Wa Gwamna Aminu Bello Masari Shawara ta Fuskar Siyasa, Alhaji Kabir Shu’aibu Charanci, shi ma a ya ajiye mukamin.
Shi kuma ya yi murabus ne domin tsayawa takarar kujerar dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Katsina ta Tsakiya.