Tony DeLuca, dan Majalisar Dokokin Amurka na jam’iyyar Democrat daga jihar Pennsylvania, wanda ya mutu a watan da ya gabata ya sake lashe kujerarsa a zaben tsakiyar wa’adin kasar.
Tsohon dan majalisar dai ya rasu ne ranar tara ga watan Oktoban da ya gabata bayan ya sha fama da gajeruwar jinya. Ya mutu ne yana da shekaru 85 a duniya.
- Ana yi wa rayuwata barazana kan sauya fasalin NNPC – Kyari
- Karin albashi: Ma’aikatan jinya za su tsunduma yajin aiki a Birtaniya
Kafar yaa labarai ta Fox News ta rawaito cewa kafin rasuwarsa, marigayin shi ne dan majalisar da ya fi dadewa a tarihin jihar.
A wani sako da ofishin jam’iyyar Democrat na Pennsylvania ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, ya ce, “Yayin da muke ci gaba da jimamin mutuwar Tony DeLuca, muna alfahari da yadda masu kada kuri’a suka ci gaba da nuna kwarin gwiwarsu a kan shi, duk da ba ya raye ta hanyar sake zabensa. Zabe na musamman zai biyo baya nan ba da jimawa ba.”
Masu sanya idanu a zaben sun ce masu kada kuri’a da dama ne suka rika zabensa da gangan, duk da sun san cewa ya rasu, saboda a sami damar gudanar da wani zaben na musamman, a maimakon su zabi abokiyar hamayyarsa.
A wani labarin kuma, akalla mutum takwas ’yan asalin Najeriya ne suka sami nasarar lashe wasu kujeru a zaben tsakiyar wa’adin da yanzu haka yake gudana a Amurkar.